Yankin Kudu maso Yamma ya fi ko ina samun mukamai a gwamnatin Buhari - Boss Mustapha

Yankin Kudu maso Yamma ya fi ko ina samun mukamai a gwamnatin Buhari - Boss Mustapha

- Tun daga shekarar 2015, an dade ana zargin cewa Shugaba Buhari ya fi rinjayar da nade-nadensa a yankin Arewa

- Wannan zargi ya sake sabunta a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da Kanal Dangiwa, wani tsohon gwamnan jihar Kaduna ya ce babu adalci a nade-naden da Buhari ya ke yi

- Sai dai wani rahoto da ya fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ya nuna cewa kashi 54.2 na nade-naden Buhari sun fito ne daga Yankin Kudu, inda Arewa ta ke da kashi 45.8

Tun daga lokacin da aka kafa gwamnatinsa a shekarar 2015, ana tuhumar shugaba Muhammadu Buhari da karkatar da muhimman nade-naden sa wajen fifita yankin Arewa inda ya fito.

Da yawan Najeriya musamman 'yan jami'yyun adawa, na tuhumar shugaba Buhari da fifita yankin Arewa fiya da na Kudu wajen yin nade-naden mukamai a gwamnatinsa.

Galibin 'yan adawar na ikirarin cewa, nade-naden mukaman da Buhari ya ke yi sun sabawa ka'aidojin da Hukumar kula da da'ar ma'aikata ta shimfida.

Haka zalika, sun hikaito sashe na 13 cikin kundin tsarin mulkin kasa, da ya shar'anta a bai wa kowane yankin kasar damar kula da al'amuran gudanarwa a ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati.

A yayin da fadar shugaban kasa da 'yan Najeriya magoya bayan Buhari suka dade su na musanta wannan zargi, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya ce salon nade-naden da ake yi a yanzu zai lalata kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna a lokacin mulkin soji, Kanal Dangiwa Umar mai ritaya, ya zargi shugaba Buhari da fifita yankin Arewa yayin nade-naden mukamai a gwamnatinsa.

A ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, Kanal Dangiwa ya zargi shugaban kasa da fifita wani yanki daya na kasar fiye da sauran a yayin nadin sabbin mukamai a gwamnatinsa.

KARANTA KUMA: Ahmed Musa, kyaftin din Super Eagles, ya bayyana motocinsa masu tsada a shafukan sada zumunta

Cikin wasikarsa mai taken: 'Shugaban kasa; ka zama na kowa da kowa', Umar ya ce salon nadin mukaman Buhari ya karkata zuwa bangare guda, kuma hakan zai iya jefa kasar a cikin rikici.

Sai dai wani rahoto da jaridar Daily Trust ta kalato daga majiya mai karfi a fadar shugaban kasa, ya nuna cewa, yankin Kudu maso Yamma ya fi ko ina samun yawan mukamai a gwamnatin Buhari.

Rahoton da ya fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ya nuna cewa kashi 54.2 cikin 100 na nade-naden Buhari sun fito ne daga Yankin Kudu, inda yankin Arewa ya samu ragowar kashi 45.8 cikin 100.

Cikin jerin nade-naden ministoci da kuma hadimai, bincike ya nuna cewa yankin Kudu maso Yamma ya ja ragamar nade-naden mukamai da kashi 33.7 cikin dari a gwamnatin Buhari.

Dalla Dalla dai ga yadda kashin nade-naden da Buhari ya yi a gwamnatinsa ya kasance daga cikin duk yankuna shida na kasar:

  1. Kudu maso Yamma - 33.7%
  2. Arewa maso Yamma - 19.5%
  3. Arewa maso Gabas - 15.3%
  4. Kudu maso Kudu - 12.6%
  5. Arewa ta Tsakiya - 11.1%
  6. Kudu maso Gabas - 7.9%

Haka zakila rahoton ya nuna cewa, shugaba Buhari ya nada mutane 64 daga Kudu maso Yamma, 37 daga Arewa maso Yamma, 29 daga Arewa maso Gabas, 24 daga Kudu maso Kudu, 21 daga Arewa ta tsakiya da kuma 15 daga Kudu maso Gabas.

A takaice dai, kashi 54.2 cikin 100 na wadanda aka nada, mutum 103 kenan, sun fito ne daga Kudancin kasar yayin da yankin Arewa ya samar da kashi 45.8 cikin dari, mutum 87 kenan.

A mahanga ta kasafin jihohi kuma, jihar Ogun ta fi ko ina samun yawan nade-naden mukamai inda ta ke mutum 17 a gwamnatin Buhari, sai kuma Adamawa a mataki na biyu da mutum 14.

Jihar Kano ta biyo baya da mutum 12, yayin da jihohin Edo, Ondo, Osun, da Katsina suka samar da mutum takwas-takwas.

Sauran jihohi masu mutum daya-daya sun hadar da Ebonyi, Imo, Bayelsa, Cross River, Filato, da kuma Zamfara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel