Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Tsohon GMD na NNPC, Maikanti Baru, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Tsohon GMD na NNPC, Maikanti Baru, rasuwa

Rahoton da muke samu da da duminsa na nuna cewa Allah ya yiwa tsohon shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Dakta Maikanti Kachalla Baru rasuwa a daren jiya.

Shugaban kamfanin ta NNPC mai ci yanzu, Mele Kyari, ya sanar da labarin rasuwarsa a shafinsa na Tuwita da safiyar nan inda ya ce marigayin ya rasu ne a daren jiya.

Yace: "Dan'uwana, abokina kuma malamina, Dakta Maikanti Kachalla Baru, tsohon GMD na NNPC, ya rasu daren jiya."

"Ya kasance mutum mai kyawawan halayen da dabi'a. Allah ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya yi masa rahama."

Asali: Legit.ng

Online view pixel