Korona: Mun fara gudanar da bincike a kan masu satar kudaden tallafi da aka bayar – ICPC

Korona: Mun fara gudanar da bincike a kan masu satar kudaden tallafi da aka bayar – ICPC

Hukumar yaki da rashawa da makamanta laifuka, ICPC ta sanar da fara binciken a kan zarge zargen rashawa da satar kudaden tallafin Coronavirus da aka tara ma gwamnati.

Daraktan ayyuka na hukumar, Akeem Lawal ne ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana ta bidiyon kallo kallo da aka yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Duk da Corona: Gwamnatin Benuwe za ta gudanar da zaben kananan hukumomi ranar Asabar

Taken taron shi ne: “COVID-19, gudanar da kudaden tallafi tare da sanya idanu a kan su”, inda yace suna binciken zargin almundahana daga bangaren wasu hukumomin gwamnati wajen rabon tallafin hatsi.

Korona: Mun fara gudanar da bincike a kan masu satar kudaden tallafi da aka bayar – ICPC
Hukumar ICPC
Asali: UGC

Sauran sun hada da zargin rashawa wajen sayo kayan tallafin COVID-19, kudaden zirga zirga da kuma kudaden da aka kashe wajen wayar da kawunan jama’a game da cutar.

Lawal ya cigaba da fadin akwai jahohin da suke binciken yadda gwamnatocinsu suka tatsi kananan hukumomi da sunan annobar, akwai kuma inda aka karkatar da kudaden tallafi.

“Duk wanda muka kama da hannu cikin badakalar nan, komai girmansa sai mun gurfanar da shi gaban kotu. Muna kuma sanda ido a kan rabon kudi da abinci a karkashin tsarin bayar da tallafin kudi na gwamnatin tarayya da kuma ciyar da dalibai.

“Dalilin shigar mu cikin harkar gudanar d kudin COVID-19 shi ne don hana rashawa da almundahana kamar yadda dokokinmu suka tanadar, haka zalika umarnin shugaban kasa ne a gare mu mu tabbatar da an yi gaskiya wajen kashe kudaden.” Inji shi.

Shi ma a jawabinsa, mashawarcin shugaban kasa a kan harkar ciyar da dalibai, Dotun Adebayo ya ce suna harin ciyar da dalibai 3,131,971 ne a karkashin tsarin.

Dotun yace kowanne gidan da aka zaba don cin moriyarsa tsarin za susamu kayan abincin N4,200 a hasashen suna da yara yan makaranta guda uku.

Kunshin abincin ya hada da kilo biyar biyar na shinkafa da wake, man gyada, man ja, gishiri, kwai guda 15 da kuma tumatirin leda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel