Kotu ta umarci a gwada kwakwalwar matar da ta zunduma diyarta cikin robar ruwa ta rufe

Kotu ta umarci a gwada kwakwalwar matar da ta zunduma diyarta cikin robar ruwa ta rufe

- Wata matashiya mai suna Oluwafunmilola Adisa ta kashe diyarta sannan ta kai kanta ofishin 'yan sanda

- Lauyan Adisa, kungiyar likitocin kwakwalwa da sauran jama'a sun bukaci a yi wa mata gwajin kwakwalwa kafin a fara sauraron shari'arta

- Adisa, mai shekaru 22, ta kashe diyarta ne bayan ta yi zargin cewa ta jawo ma ta karin wahala a rayuwarta

Wata kotun majistare da ke zamanta a yankin Igbosere a garin Legas ta umarci a gudanar da gwajin kwakwalwa a kan wata matashiya, Oluwafunmilola Adisa, wacce ta kashe diyarta ta hanyar tsundumata da rufeta a cikin robar ajiyar ruwa.

Kotun ta umarci a gudanar da gwaji a kan Adisa a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas.

Lauyan da ke kare matashiyar ne ya bukaci kotu ta yi aiki da sashe na 217(3) na kundin dokokin manyan laifuka na shekarar 2015, wanda ya bukaci a gudanar da gwajin kwakwalwa domin sanin koshin lafiyar hankalin wacce ake kara.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Adisa ta kashe diyarta, sannan ta rubuta wasika zuwa ga 'yar uwarta tare da sanar da ita yadda ta kashe jaririyar a gidansu da ke rukunin gidajen Gowon a unguwar Ipaja.

Bayan ta aikawa 'yar uwarta wasika, Adisa ta wuce zuwa ofishin 'yan sanda tare da kai rahoton abinda ta aikata.

Kotu ta umarci a gwada kwakwalwar matar da ta zunduma diyarta cikin robar ruwa ta rufe
Kotu ta umarci a gwada kwakwalwar matar da ta zunduma diyarta cikin robar ruwa ta rufe
Source: UGC

Adisa, mai shekaru 22, ta kashe diyarta ne bayan ta zargeta da zama silar wahalhalun da ta ke sha a rayuwa.

Kungiyoyi ma su zaman kansu, shugaban kungiyar likitocin kwakwalwa na Najeriya, Taiwo Sheikh, da shugaban kungiyar kare hakkin fursunoni, Ahmed Adetola-Kazeem, sun bukaci a yi wa Adisa gwajin kwakwalwa.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto

Sun yi zargin cewa Adisa na fama da sarkewar tunani da dusashewar aikin kwakwalwa sakamakon haihuwar da ta yi watanni 21 da su ka gabata.

Yayin zaman kotun na ranar Laraba, mai shari'a, Dora Ojo, ya amince da bukatar lauyan da ke kare Adisa.

Ya umarci a yi wa Adisa gwajim kwakwalwa a asibitin koyarwa na jami'ar Legas tare da daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel