Hedkwatar tsaro ta aike sakon gaggawa ga jihohin Arewa na tsakiya da Arewa maso yamma

Hedkwatar tsaro ta aike sakon gaggawa ga jihohin Arewa na tsakiya da Arewa maso yamma

Sakamakon ci gaban ruwan wutar da dakarun sojin Najeriya ke yi wa 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma da yankin arewa ta tsakiya, hedkwatar tsaro ta ce akwai yuwuwar 'yan bindigar su fara tserewa daga jihohin.

A don haka ne headkwatar tsaron ke tabbatar wa da jama'a cewa an dauka matakai idan hakan ta faru don shawo kan matsalar.

A don haka ne hedkwatar tsaro ta kasar baki daya ta tura dakarun sojin sama zuwa jihohin Kaduna, Niger, Nasarawa da Kogi.

Kamar yadda hedkwatar tsaron ta bayyana, a shirye take don shawo kan dukkan matsalar tsaro da ta addabi yankin.

"A shirye hedkwatar tsaron take da ta bai wa yankin dukkan tsaron da ya kamata don shawo kan ta'addanci," takardar tace.

Ta kara da yin kira ga jama'a da su kai rahoton duk wani mutum ko wani al'amari da basu yarda dashi ba don tallafawa jami'an tsaro.

"Muna kira ga jama'a da su garzaya ga hukuma ko jami'an tsaro don mika rahoton duk wani al'amari ko mutum da basu yarda dashi ba," takardar ta kara da cewa.

Hedkwatar tsaro ta aike sakon gaggawa ga jihohin Arewa na tsakiya da Arewa maso yamma
Hedkwatar tsaro ta aike sakon gaggawa ga jihohin Arewa na tsakiya da Arewa maso yamma. Hoto daga Informationng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)

A wani labari na daban, kamar yadda rahotanni daga jihar Sokoto suka bayyana, an kashe mutum kusan 60 a cikin wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2020 a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabon-Birnin-Gobir.

Ganau ba jiyau ba, sun ce maharan sun dauki tsawon sa'o'i suna ruwan wuta a kauyukan ba tare da kowa ya tunkaresu ba.

Hakazalika, wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin da suka kai karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.

Wani jami'in da ya samu zuwa inda al'amarin ya faru, ya sanar da BBC cewa, da misalin karfe uku zuwa biyar na yammacin Laraba ne suka samu labarin cewa mutane sun taso da babura kusan 100 daga daji.

Mutanen sun taho ne daga dajin da ke kusa da Issa sannan sun nufi kauyukan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng