Korona: Mutane 276 un karu a Najeriya, 19 a Kaduna, 4 a Kano

Korona: Mutane 276 un karu a Najeriya, 19 a Kaduna, 4 a Kano

Hukumar NCDC ta fitar da sanarwar samun sabbin mutane 278 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar korona a fadin Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana tun bayan bullar annobar korona a Najeriya, jimillar ma su dauke da cutar korona a Najeriya ya haura dubu takwas.

Alkaluman NCDC na ranar Talata sun nuna jerin jihohi da adadin mutanen da kowacce ta samu daga cikin jimillar ma su dauke da cutar kamar haka;

Lagos-161

Rivers-36

Edo-27

Kaduna-19

Nasarawa-10

Oyo-6

Kano-4

Delta-3

Ebonyi-3

Gombe-2

Ogun-1

Ondo-1

Borno-1

Abia-1

Bauchi-1

A cewar NCDC, akwai jimillar mutum 8344 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar korona a Najeriya, ya zuwa karfe 11:30 na daren ranar Talata.

An sallami jimillar mutane 2385 daga cibiyoyin killacewa daban-daban da ke fadin kasar nan bayan an tabbatar da cewa sun warke sarai.

Mutane 249 ne suka mutu sakamakon kamuwa da kwayar cutar korona, a cewar alkaluman hukumar NCDC na ranar 26 ga watan Mayu.

DUBA WANNAN: Abba Kyari: Buhari bai taba mika ikon ofishinsa ga kowa ba - Fadar Shugaban kasa

A wani labarin mai nasaba da annobar korona, Legit.ng Hausa ta wallafa cewa Faifan bidiyon yadda wata mata ta cika da murna bayan an ba ta gado a cibiyar killace ma su cutar korona ya bawa jama'a a mamaki.

A cikin faifan bidiyon, wanda ya yi farin jini a dandalin sada zumunta, matar ta nuna gadonta a cikin dogon da ake killace ta tare da sauran ma su cutar korona.

Duk da ba ta bayyana wurin da cibiyar ta ke ba, matar ta nunawa mabiyanta a dandalin sada zumunta gadon da ta aka ba ta.

Matar ta kasance cikin farin ciki da jin dadi yayin da ta ke nadar faifan bidiyon gadonta tare da bayyana cewa har na'urar sanyaya daki.

"Nan ne cibiyar killacewa, kun gani, har da na'urar sanyaya daki. Wannan ne gadona, shine gadona, gadona ne," kamar yadda matar ke fada cikin farin ciki da jin dadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng