Ganduje ya yi martani a kan labarin lalacewar kayan abincin da FG ta tura wa Kano

Ganduje ya yi martani a kan labarin lalacewar kayan abincin da FG ta tura wa Kano

Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta musanta rade-radin da ake yi na cewa ta yi watsi da kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta ba jihar har ruwan sama ya lalata.

kamar yadda kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba, ya aika wa manema labarai a yau Talata, ya ce ba gaskiya bane zargin. Ya ce kayan na nan babu abinda ya lalace sakamakon dukan ruwan saman.

"Gwamnatin jihar Kano tana sanar da yin watsi da rahotannin da wasu masu bakar aniya ke yadawa cewa na bar hatsin da gwamnatin tarayya ta turo Kano a makonni biyu da suka gabata har ruwa yayi musu duka.

"An turo hatsin ne a matsayin tallafi don rage radadin korona ga matalauta da mabukata a jihar," sanarwar tace.

Kwamishinan ya kara da cewa, tun kafin a kawo tallafin, ruwan sama ya dade da sauka a Kano kuma gwamnatin ta dauka matakin rufe hatsin da tamfol don hana su lalacewa.

Kamar yadda yace, kwamitin da aka dora wa alhakin tattara tallafin cutar korona din ya fara shirin rarraba kayan abinci ga talakawan.

Ganduje ya yi martani a kan labarin lalacewar kayan abincin da FG ta tura wa Kano
Ganduje ya yi martani a kan labarin lalacewar kayan abincin da FG ta tura wa Kano. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: MNJTF sun ragargaza mayakan ta'addanci ta jiragen yaki

A wani labari na daban, a kalla mutum 600, wadanda suka hada da mata da kananan yara 'yan bindiga suka fatattaka a fadin jihar Katsina sannan suka samu masauki a filin kwallo da ke ATC a Katsina.

'Yan gudun hijira masu tarin yawa na ci gaba da tururuwa zuwa filin kwallon inda suke kira ga jama'a don kai musu tallafin abinci.

'Yan gudun hijirar na ci gaba da tururuwar samun mafaka a cikin wasu sassa na jihar Katsina. A kalla mutane 400 ne suka samu masauki a garejin kanikawa na Bebeji inda mutum 360 suka samu mafaka a Yammawa.

Hakazalika, sama da mutum 100 ne suka samu mafaka a Tudun Baras. Tsanantar hare-haren 'yan bindiga da ya addabi jama'ar kananan hukumomin Batsari, Safana, Jibia, Kankara, Dandume, Faskari da Sabuwa ya hana mazauna yakin da dama zaman gidajensu.

Idan za mu tuna, gwamnatin jihar Katsina ta shiga tattaunawa da 'yan bindigar da suka addabi yankin, tare da alkawarin rangwame garesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel