Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)

Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)

Dapchi, babban birnin karamar hukumar Bursari ta jihar Yobe ta zama kufai bayan harin da 'yan ta'adda suka kai wa jama'ar garin.

Da yawa daga cikin mazauna garin sun yi shagalin bikin salla karama ne a daji da kauyuka makusanta sakamakon tsoron da ya shiga zukatansu.

Wani mazaunin garin wanda ya zanta da SaharaReporters ya ce, "Zan iya kirga yawan jama'ar da ke Dapchi. Ba mu da yawa. Mutane duk sun tsere don samun mafaka. Su kan shigo amma suna komawa maboyarsu."

A makon da ya gabata ne mayakan ta'addancin suka dinga kai hari garin Dapchi inda suka kurmushe asibiti da fadar hakimi.

A halin yanzu, an daina bin hanyar Dapchi zuwa Damaturu saboda tsoron harin 'yan Boko Haram.

Jama'a daga arewacin jihar Yobe da ke tafiya zuwa garin Damaturu sai dai su bi ta garin Potiskum don zuwa inda suka nufa.

Jama'ar kananan hukumomin Bursari da Tarmuwa sun fada tsananin tsoro sakamakon harin mayakan ta'addancin.

Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sake tsawaita dokar hana zirga-zirga (Bidiyo)

Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel