Dumu-dumu: An kama masu hakar kabari da kan mutum 5

Dumu-dumu: An kama masu hakar kabari da kan mutum 5

Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta kama maza hudu dauke da kawunan mutum biyar. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tee Leo Ikoro, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa ana ci gaba da bincikar lamarin tare da bankado masu hannu a ciki.

Wadanda ake zargin duk masu hakar kabari ne, kuma sun shiga hannu ne a ranar Litinin bayan fito da wata gawa da aka birne bayan kwanaki biyu da suka yi.

An gano sunan mutanen da Oluwadare Idowu mai shekaru 67, Adewale Abiodun mai shekaru 40, Akinola Sunday mai shekaru 69 da kuma Seun Olomofe mai shekaru 45.

Lamarin ya faru ne a wata makabarta da ke karamar hukumar Akure ta yamma a jihar Ondo inda wadanda ake zargin suke aiki.

Wasu daga cikin 'yan uwan mamacin ne suka je makabartar don yin kankare a kabarin dan uwansu, amma sai suka gane cewa an cire kan gawar dan uwan nasu.

Ba su jinkirta ba suka garzaya wurin 'yan sanda inda aka zo tare da kama wadanda ake zargin.

A yayin kamen, an gano cewa 'yan sandan sun samu kawunan mutum hudu wadanda aka hako daga kabari a tare da wadanda ake zargin.

Dumu-dumu: An kama masu hakar kabari da kan mutum 5
Dumu-dumu: An kama masu hakar kabari da kan mutum 5. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Idi: Buhari da gwamnoni sun kulla yarjejeniya biyar a kan bude masallatai

A wani labari na daban, a kalla mutum 600, wadanda suka hada da mata da kananan yara 'yan bindiga suka fatattaka a fadin jihar Katsina sannan suka samu masauki a filin kwallo da ke ATC a Katsina.

'Yan gudun hijira masu tarin yawa na ci gaba da tururuwa zuwa filin kwallon inda suke kira ga jama'a don kai musu tallafin abinci. 'Yan gudun hijirar na ci gaba da tururuwar samun mafaka a cikin wasu sassa na jihar Katsina.

A kalla mutane 400 ne suka samu masauki a garejin kanikawa na Bebeji inda mutum 360 suka samu mafaka a Yammawa. Hakazalika, sama da mutum 100 ne suka samu mafaka a Tudun Baras.

Tsanantar hare-haren 'yan bindiga da ya addabi jama'ar kananan hukumomin Batsari, Safana, Jibia, Kankara, Dandume, Faskari da Sabuwa ya hana mazauna yakin da dama zaman gidajensu.

Idan za mu tuna, gwamnatin jihar Katsina ta shiga tattaunawa da 'yan bindigar da suka addabi yankin, tare da alkawarin rangwame garesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel