Ma su cin moriyar shirin N-Power sun tankawa minista Sadiya a kan biyan alawus din watan Afrilu

Ma su cin moriyar shirin N-Power sun tankawa minista Sadiya a kan biyan alawus din watan Afrilu

- Ma su cin moriyar shirin N-Power sun bayyana rashin amincewarsu da kalaman Sadiya Umar Farouk

- A ranar Asabar ne Sadiya Umar Farouq, ministar ma'aikatar walwala, jin kai da bayar da tallafi, ta sanar da cewa an kammala biyan alawus din 'yan N-Power na watan Afrilu

Dumbin ma su cin moriyar shirin tallafawa matasan da su ka kammala karatu, wato N-Power, sun bayyana cewa har yanzu ba a biyasu alawus dinsu na watan Afrilu ba, wanda hakan ya saba da kalaman ministar ma'aikatar jin kai, bayar da tallafi da walwala, Sadiya Umar Farouq.

A ranar Asabar ne ministar ta sanar da cewa an biya dukkan ma su cin moriyar shirin N-Power alawus dinsu na watan Afrilu.

Kazalika, ta sanar da cewa za a yi wa shirin garambawul bayan an biya ma su cin moriyar shirin alawus dinsu na watan Mayu.

Da ta ke bayani a kan dalilin samun jinkiri wajen biyan alawus din masu cin moriyar shirin, Sadiya ta ce ma'aikatarta ta samu 'yar tangarda da tsarin 'GIFMIS' da gwamnatin tarayya ke amfani da shi wajen biyan ma su cin moriyar shirin alawus dinsu.

Ma su cin moriyar shirin N-Power sun tankawa minista Sadiya a kan biyan alawus din watan Afrilu
Sadiya Umar Faruk
Asali: UGC

Ministar na wannan bayani ne bayan ma su cin moriyar shirin N-Power sun mamaye kafafen sada zumunta da korafin an ki biyansu alawus dinsu na watan Afrilu a daidai lokacin da aka saka dokar kulle saboda annobar korona.

"Mun samu wasu 'yan matsaloli da tsarin GIFMIS, wanda hakan ya haifar mana da jinkiri wajen biyan alawus, amma yanzu ina mai sanar da cewa mun biya dukkan 'yan N-Power; na rukunin A da na rukunin B, alawus dinsu na watan Afrilu," a cewarta.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 1000 - Buratai

Sai dai, bayan sanarwar ministar, dumbin 'yan N-Power, da Premiumtimes ta gana da su ta wayar tarho da wadanda su ka bayyana ra'ayinsu a dandalin sada zumunta, ba su amince da kalaman ministar ba, tare da bayyana cewa ba a biyasu ba har yanzu.

Ma su cin moriyar shirin sun bukaci ministar ta yi murabus saboda wahalar da su ke sha sakamakon jinkirin da ake samu wajen biyansu alawus tun bayan mayar da shirin karkashin ofishinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng