Hotunan Buhari yayin Sallar Idi cikin jam'i, ya sha 'selfie' da 'yayansa a cikin gida
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga jerin sahun sauran Musulman Najeriya wajen gudanar da Sallar Idi bayan kammala azumin watan Ramadana.
A hotunan da shugaba Buhari da kansa ya wallafa a shafinsa na tuwita jim kadan bayan kammala Sallar Idi, ya ce "ina taya kowa murnar Idi".
"A yayin da mu ka kammala azumin Ramadan cikin nasara, kuma mu ke gudanar da murnar Eid-el-Fitr cikin takatsantsan saboda yanayin da ake ciki, akwai bukatar mu cigaba da riko da aiyukan alheri har gaba da wannan lokaci na bikin Sallah. Ina yi wa dukkan jama'a barka Sallah," a cewar takaitaccen sakon da Buhari ya wallafa.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A ranar Juma'a, 23 ga watan Mayu, shugaba Buhari da kungiyar gwamnoni sun yi taro inda suka amince da bude wuraren bauta tare da yin sallar jam'i amma kada a zarta mutum 50.
Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya tabbatar da cewa yin taron ya hada har da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN).
Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnoni shida na yankin arewa da suka hada da Gwamna Ganduje na jihar Kano sun dage dokar hana jam'i a jihar don samu a yi sallar Idi.
DUBA WANNAN: Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Sakon Atiku Abubakar
Jama'a da yawa sun kalubalanci wannan matakin don ya saba wa shawarar kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona da kuma hukumar NCDC.
Gwamna Umar Ganduje na jihar Kano ya shawarci malaman addinin islama a jihar da su gabatar da gajeriyar huduba yayin sallar idi wacce ya aminta da a yi duk da gwamnatin tarayya ta soki hakan.
A wata takarda da sakataren yada labaran gwamnan ya fitar a ranar Asabar, Abba Anwar ya ce za a yi sallar idi a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.
Ya ce dole ne Musulmi su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka tanadar don sallar jam'i.
Sai dai, a wasu hotunan Sallar Idi daga Masallacin unguwar Bompai a cikin Kano da jaridar Daily Trust ta wallafa, jama'a sun gudanar da Sallah cikin jam'i ba tare da kiyaye dokar nesanta ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng