Lamarin ganin wata ko rashin gani: Jayayya Marar Malili - Daga Dr. Ibrahim Umar Disina

Lamarin ganin wata ko rashin gani: Jayayya Marar Malili - Daga Dr. Ibrahim Umar Disina

Tsokacin Edita: Dukkan abin da zaku karanta a nan ra'ayin marubuci ne kuma ba ra'ayin Legit.ng ba

(1) Ibadar duban wata an rataya ta ne da shugabanci, Sahabbai in sun gani Annabi suke fadawa shi kuma ya sanar, A zamanin yau ne wanda ya gani yake yin gaban kansa.

(2) Jagoran Musulmai a Nigeria shine Sultan, Yace ba'a sami tabbacecciyar hanya kan anga Wata ba, Yau 30 Ramadan.

(3) Ba dole ba ne don mutam ya bayar da shaidar ganin wata a karba, Ba adalci kadai ake dubawa akwai yiwuwar ganinsa, Musamman ma kasa irin tawa da ko ran 27 akace a duba sai an sami mai ganinsa. Kowace kasa tana ki ko karba, amma a kasata in akaki karba ya zama abin yamadidi.

(4) Hadin kan Musulmai yafi mahimmanci sama da ganin jinjirin wata!!

(5) Yau kudanci da yammacin Nageria sunce suna bayan Sultan, Yayin da arewaci ke kwaye masa baya!!

(7) Shugabannin kungiyoyi addini kan yi gaban kansu don fitowa a matsayin Jarumai amma suna yiwa kansu da Al'ummar Musulmai raunin da baya jin magani!!

(8) In bera da sata.... Kwamitocin ganin wata suna gagarumin aiki amma al'ummarsu ba su san yanda su ke namijin aiki ba gabanin isa matsaya ta karshe , information is power!!

(8) Tun Jiya wasu sun sabawa sauran Musulmai sunyi sallah, Ba abin mamaki ba ne don sunyi hakan, irin nasu tsarin kenan; Sabawa sauran Musulmai!! Yau kuma wassu sunce kar a yi Azumi amma gobe a hau Idi, kamar tilasta musu akeyi sai sun sabawa sauran Musulmai.

(9) Masu falaki kuwaa cewa sukeyi an haifi jinjirin wata 6:39 Agogon Abuja, Rana kuma ta fadi 6:46, wato a Nigeria anga watan tun gabanin a Haifeshi!! Wani aiki sai kasata!!

(10) Magidanta lissafin cefene ya canza sai hakuri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel