Tsohon alkalin kotun kolin Najeriya, Karibi, ya rasu
Tsohon alkalin kotun koli, Adolphus Karibi-Whyte ya rasu yana da shekaru 88. Dan alkalin, Dagogo Karibi-Whyte ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa a garin Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
An haifa dan asalin Abonnema din da ke jihar Rivers a ranar 29 ga watan Janairun 1932.
Ya halarci kwalejin Kalabari da ke Buguma a jihar Rivers daga 1946 zuwa 1959 kuma ya yi aiki a matsayin kilakin kotu daga 1951 zuwa 1957.
Ya samu digirinsa a fannin shari'a daga jami'ar Hull da ke Ingila a 1960 kuma an rantsar da shi a matsayin lauya a shekarar da ta zagayo.
A watan Satumban 1962, ya samu digirinsa na biyu a fannin shari'a daga jami'ar Landan. A shekarar 1970 ya samu digirin-digirgir a fannin shari'a daga jami'ar jihar Legas.
An nada marigayin a matsayin alkalin kotun hukumar kudin shiga ta tarayya a 1976.
An kara masa matsayi zuwa kotun daukaka kara a 1980 kuma daga baya ya koma kotun kolin Najeriya a 1984.
Wasu daga cikin manyan shari'un da ya yanke hukunci kuma ya samu jinjina a Najeriya sun hada da: Shari'ar gwamnatin jihar Gongola da Tukur a 1989, shari'ar Antoni janar din tarayya da Antoni Janar din jihar Abia.

Asali: Twitter
KU KARANTA: An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi
Ya yi shari'ar Grace Jack da jami'ar aikin noma da ke Makurdi a 2004 da kuma shari'ar bankin Savannah da Pan Atlantic shipping da Transport Agencies Limited a 1987.
Tsohon alkalin ya rasu ya bar 'ya'ya bakwai.
A wani labari na daban, Sheikh Bello yabo dan asalin jihar Sokoto ya shiga hannun jami'an tsaro tun bayan bazuwar bidiyon da ya caccaki gwamnan Kaduna a kan hana sallar Idi.
A wani sautin murya mai tsayin kusan minti biyar, malamin addinin Islama mai suna Sheikh Bello Yabo, ya caccaki Gwamna Malam Nasir El-Rufai saboda hana sallar Idi da yayi a jihar Kaduna.
A sautin muryar, ya yi kira ga Musulmi da su bijirewa hukumomi a kowanne gari da aka hana su fita sallar Idin karamar sallar don dakile yaduwar cutar korona, kamar yadda jaridar SaharaReporters ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng