Yanzu-yanzu: An samu karin mutum 245 masu korona a Najeriya, jimilla ta kai 7261

Yanzu-yanzu: An samu karin mutum 245 masu korona a Najeriya, jimilla ta kai 7261

A yau Juma'a, 22 ga watan Mayun 2020, alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC) sun bayyana cewa an samu karin mutum 245 masu dauke da kwayar cutar korona a fadin kasar nan.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, jihar Legas ta samu karin mutum 131, jihar Jigawa ta samu karin mutum 16 sai jihar Ogun da ta samu karin mutum 13 da ke dauke da cutar.

Hakazalika, jihar Borno ta samu karin mutum 9 da ke dauke da muguwar cutar, jihar Oyo, Rivers da Ebonyi suna da karin mutum tara-tara.

Babbar cibiyar kasuwancin arewa, wato jihar Kano, ta samu karin mutum 8 da ke dauke da cutar. Jihar Kwara na da karin mutum 7 sai jihar Katsina mai karin mutum 5.

Jihohin Akwa Ibom da Sokoto sun samu karin mutum uku-uku yayin da jihohin Bauchi da Yobe ke da karin mutum bibbiyu.

Jihohin Anambra, Gombe, Niger, Ondo, Filato, Abuja da Bayelsa na da karin mutum daddaya.

Jimillar masu dauke da kwayar cutar a Najeriya sun kai 7261. An sallama mutum 2007 daga asibiti bayan sun warke, yayin da mutum 221 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel