Yanzu-yanzu: Mun gano dalilin mace-mace a arewacin Najeriya - Dr Gwarzo

Yanzu-yanzu: Mun gano dalilin mace-mace a arewacin Najeriya - Dr Gwarzo

Tawagar kwararrun da gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura yankin arewacin kasar nan domin bankado dalilin mace-mace a wasu jihohin yankin ta ce ta fara gano dalilin.

Kamar yadda tawagar ta bayyana, ta kasa mace-macen gida bakwai kuma yanzu tana gab da kammala rangadin da take yi a jihohin, inda daga bisani za ta fitar da bayanai.

Dr Nasiru Sani Gwarzo, wanda shine shugaban kwamitin ya ce kawo yanzu, sun ziyarci jihohi shida daga cikin takwas da aka fuskanci mace-macen jama'a a watan jiya.

Dr Gwarzo ya kara da cewa sun gano abubuwa da yawa game da mutuwar ta farat ɗaya da mutane suka rinka yi a jihohin arewacin kasar.

Gwarzo ya ce sun gano abubuwa da dama game da mutuwar farat daya da jama'a ke yi a jihohin arewacin Najeriyan.

"Hatta makabartun mun kai wa ziyara inda muka kidaya kaburburan jama'a kuma 'yan uwansu sunyi mana bayanai kan mamatansu.

"Sai dai kuma, mun gano cewa wasu jihohin na zuzuta al'amuran. Mun kara da samun samfurin mamatan a jihohinsu kuma muna jira sakamakon gwajin," Gwarzo yace.

Yanzu-yanzu: Mun gano dalilin mace-mace a arewacin Najeriya - Dr Gwarzo
Yanzu-yanzu: Mun gano dalilin mace-mace a arewacin Najeriya - Dr Gwarzo. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

A wani labari na daban, majalisar malaman jihar Kano ta ce kamata yayi gwamnati ta yi tunani kafin yanke hukuncin dawo da gabatar da sallar Juma'a da idi a jihar saboda yuwuwar yaduwar cutar korona.

Mallam Ibrahim Khalil, shugaban kungiyar majalisar malaman Kano, ya sanar da BBC cewa gwamnatin jihar ba ta tuntubesu ba a yayin yanke wannan hukuncin nata. Amma ya kamata a ce ta yi la'akari da bukatar jama'a.

Kamar yadda malamin ya bayyana, ya ce ya zama dole a kan gwamnati ta duba damuwar jama'arta da kuma abinda ya dace, tunda bata tuntubi majalisar malamai ba.

A cewarsa, "Amma irin wannan yanayi na annoba da ake ciki, duk wanda yake jin tsoron cewar zai kamu da cutar idan yaje masallacin ko kuma zai zama hadari, to zai iya zamansa a gida."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel