Abin da yasa Coronavirus ta fi kashe masu kudi a Najeriya – Ministan kiwon lafiya

Abin da yasa Coronavirus ta fi kashe masu kudi a Najeriya – Ministan kiwon lafiya

Ministan kiwon lafiya a gwamnatin Buhari, Osagie Ehanire ya ce gwamnati ta damu kwarai da yadda manyan mutane masu ilimi ke mutuwa dalilin cutar Coronavirus.

Punch ta ruwaito ministan ya bayyana dalili, inda yace masu kudin sun gwammace a kula dasu a gidajensu a kan su tafi cibiyoyin kulawa da masu cutar, sai lamari ya baci ake kai su asibiti.

KU KARANTA: Dan tsaro ba tsoro ba: Gwamnati ta girke zaratan Sojoji masu jiran ko-ta-kwana a jahar Filato

Osagie ya bayyana haka ne yayin taron manema labaru da kwamitin yaki da COVID-19 a Najeriya ta shirya a garin Abuja, a ranar Talata, inda ya baiwa masu dauke da cutar shawara.

Ministan ya yi kira a garesu dasu bi umarnin likitoci wajen shan magani ba son ran su ba.

A yanzu haka cibiyoyin bincike 5 suna aiki a kan magungunan COVID-19, daga cikinsu har da Chloroquine.

Abin da yasa Coronavirus ta fi kashe masu kudi a Najeriya – Ministan kiwon lafiya
Ministan kiwon lafiya Hoto: Twitter
Asali: Twitter

“Yayin da muke kara samun ilimi a kan Coronavirus a kullum, dole ne mu dinga gyara dabarun yaki da shi, uwa ranar Litinin mun samu mace macen mutane 191 a jahohi 26 da Abuja.

“Duk da cewa yawan mace macen basu kai na wasu kasashe ba, amma akwai damuwa saboda yawancin su masu ilimi ne kuma manyan mutane ne da suka gwammace samun kulawa daga gida, ba’a tashi kai su asibiti sai ta yi kamari, kuma suna tattare da cututtuka daban daban dama.

“Duba da yanayin cutar, masu dauke da ita ka iya fuskantar matsala cikin kankanin lokaci, wannan yasa akwai bukatar kowa ya nemi kulawar da ta dace da zarar an tabbatar yana dauke da cutar.” Inji shi.

Daga karshe ministan yace suna aikin zagayen cibiyoyin killace masu cutar, zuwa yanzu sun je Yenagoa a jahar Bayelsa da Osogbo na jahar Osun State, kuma zasu cigaba da taimaka musu.

A wani labari kuma, saboda karancin kudaden shiga, hukuma kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya, FAAN ta bayyana cewa ba lallai bane ta iya biyan cikakken albashin ma’aikatanta.

Hukumar ta bayyana cewa ma’aikata za su fuskanci canji a albashinsu daga watan Mayu, amma da zarar jirage sun cigaba da tashi za ta cigaba da biyansu cikakkun hakkokinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel