Almajiranci: Arewa na dawowa da kudu dawainiyar da ke kanta - Ohanaeze

Almajiranci: Arewa na dawowa da kudu dawainiyar da ke kanta - Ohanaeze

Uche Achi-Okpaga, sakataren yada labarai na Ohanaeze Ndigbo, ya zargi shugabannin arewa da dora wa yankin kudu nauyin almajiran jihar.

A wata tattaunawar da yayi da jaridar The Punch, Achi-Okpaga ya zargi shugabannin yankin da kirkiro matsala a tsakaninsu ta hanyar mayar da almajiran jihohinsu.

Sau da yawa, kananan yara masu shekaru tsakanin hudu zuwa 15 ake tura su wurin malamai masana ilimin Qur'ani don neman ilimi.

Da yawa daga cikinsu na karewa da bara don samun abinci da sadaka don kuwa malaman basu iya ciyar dasu.

Tun bayan barkewar annobar Coronavirus, wasu gwamnonin a yankin arewa sun dinga mayar da almajirai jihohinsu.

Mai magana da yawun Ohanaeze yace, wannan ya saba dokar hana shige da fice tsakanin jihohi. Ya kara da cewa barin almajiran a inda suke ya fi a maimakon mayar dasu jihohinsu na asali.

Almajiranci: Arewa na dawowa da kudu dawainiyar da ke kanta - Ohanaeze
Almajiranci: Arewa na dawowa da kudu dawainiyar da ke kanta - Ohanaeze. Hoto daga Getty Images
Source: UGC

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriyasun tarwatsa ma'adanar makaman 'yan ta'adda a Borno, sun bi ta wani da motar yaki (Bidiyo)

"Kungiyar kabilar Igbo ta matukar damuwa da yadda almajirai ke ci gaba da shiga yankin kudancin Najeriya," yace.

"Amma kuma, wannan matsalar na da fuskoki da yawa. Idan zamu tuna, a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ne aka gina makarantun almajirai. Tuntuni 'yan arewa ke mulki amma basu taba wannan tunanin ba.

"Duk da cewa Jonathan ya gina musu makarantu amma basu taba tunanin hakan zai zama babbar matsala ga arewa a gaba ba.

"Almajiran na tafe da yawansu a cikin manyan motoci. Tambayar ita ce, su waye ke samar da motocin? Almajiran da muka sani basu da kudi kuma ba za su iya samar da motocin tafiye-tafiye ba," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, farmakin da sojin saman Najeriya karkashin rundunar Operation Lafiya Dole ta kai a Njimia da ke dajin Sambisa, ya tarwatsa kayan yakin 'yan ta'addan Boko Haram.

Hari ta jiragen saman yakin da dakarun suka kai a ranar Talata ya biyo bayan rahotannin sirrin da suka samu a kan makaman 'ya ta'addan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel