Dalilin da yasa Abacha ya boye kudade a kasashen waje - Buba Galadima

Dalilin da yasa Abacha ya boye kudade a kasashen waje - Buba Galadima

Tsohon aminin shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya ce shawara aka baiwa tsohon shugaban kasan mulkin soja, Sani Abacha, ya boye makudan kudade a kasar waje.

Za ku tuna cewa a makon da ya gabata gwamnatin tarayya ta karbo kudi $311 million daga kasar Amurka da Jersey da ake zargin marigayi Abacha da wawura.

Kimanin kudin baitul malin Najeriya dalar Amurka Bilyan 5 ($5 billion) aka wawure lokacin mulkin Abacha ba tare da sanin gwamnati ba.

Lissafi ya nuna cewa kudaden da Abacha ya wawura da aka samu damar dawo dasu yanzu sun kai $3.624 billion.

A hira da yayi da jaridar The Nation, Injiniya Buba Galadima, wanda babban jami'in gwamnati ne lokacin Abacha ya bayyana ainihin dalilin da yasa Abacha ya boye kudadenn.

Ya ce yawancin mutanen da ke cewa Marigayi Janar Sani Abacha sace kudin yayi basu da ilimin abinda suke fadi shiyasa.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5

A cewar Galadima "Ni ina da wata fahimta daban game da abinda kuke kira 'Badakalar Abacha'."

"Abinda na sani sarai shine a lokacin, wasu manyan jami'an gwamnati sun san da kudin da ake boyewa kuma sun san shawara wasu takwarorinsa, shugabannin kasashe suka bashi."

"Saddam Hussein na daya daga cikinsu. Muammar Gaddafi na cikinsu."

"Sun bashi shawarar cewa akwai yiwuwan Amurka ta kakabawa Najeriya takunkumi saboda haka ya boye wasu kudade a wajen Najeriya, da zai iya ciyar da kasar na tsawon akalla watanni shida, saboda idan Amurka ta daskarar da asusun Najeriya, ba za a wahala ba."

"Ni babba ne a gwamnatin. Ina daya daga cikin wadanda ake kira 'yaran Abacha. Ni ne Dirakta Janar na hukumar sufurin ruwa, inda shiga da fitan kayayyaki irinsu man fetur karkashina yake."

"Saboda haka ina da ta cewa game kudin da ake ikirarin Abacha ya sace."

Ga jerin kudaden da aka dama amsowa kawo yanzu:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a akwatin: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel