Darus Salam: Sabuwar kungiyar ta'addanci da ta sauka a Arewa

Darus Salam: Sabuwar kungiyar ta'addanci da ta sauka a Arewa

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sanar da isowar wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Darus Salam jiharsa, wacce ya kwatanta da kungiya mai tarin hadari.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jihar Nasarawa na cikin matsanancin halin matsalar tsaro a cikin kwanakin nan.

Sabuwar kungiyar ta kware a garkuwa da manyan mutane na jihar kamar su mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar, sarakuna, sakatarorin gwamnati da sauransu.

A yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan ya danganta garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen da ake da kungiyar.

Kamar yadda yace, da farko kungiyar ta bar jihar amma da ta tashi dawowa sai ta iso da sabon karfinta inda ta sauka a wasu kananan hukumomi na jihar.

Gwamna Sule ya yi kira ga Shugaban Buhari da ya tura jami'an tsaro jihar don shawo kan lamarin.

Darus Salam: Sabuwar kungiyar ta'addanci da ta sauka a Arewa
Darus Salam: Sabuwar kungiyar ta'addanci da ta sauka a Arewa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Adadin 'yan ta'addan da dakarun Najeriya suka halaka a daren jiya - Rundunar soji

"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo mana dauki a fannin tsaro a yankin, karin jami'an 'yan sanda zai iya sa su gaggauta barin jihar.

"Halin da karamar hukumar Toto ke ciki ya kazanta a halin yanzu. Rundunar sojin Najeriya ta kokarta tare da 'yan sanda a kwanaki inda suka tarwatsa sansanin kungiyar Darus Salam din. Amma sun kara kafa wani.

"A halin yanzu suna garkuwa da mutane tare da kashe-kashe. Al'amarin ya kazanta kuma ina tunanin jami'an tsaro za su iya shawo kai," Gwamnan ya sanar.

A wani labari na daban, kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce dakarun sojin Najeriya sun halaka mayakan ta'addanci na Boko Haram tara a Mainok da ke jihar Borno.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa dakarun da mayakan ta'addancin sun yi musayar wuta a daren Laraba, 13 ga watan Mayu.

Sagir Musa, kakakin rundunar sojin a wata takarda da ya fitar, ya ce sun yi nasarar kwace wasu motocin yaki daga 'yan ta'addan.

Sai dai cike da alhini, ya sanar da cewa dakarun Najeriya biyu sun samu kananan raunika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel