Adadin 'yan ta'addan da dakarun Najeriya suka halaka a daren jiya - Rundunar soji

Adadin 'yan ta'addan da dakarun Najeriya suka halaka a daren jiya - Rundunar soji

Kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce dakarun sojin Najeriya sun halaka mayakan ta'addanci na Boko Haram tara a Mainok da ke jihar Borno.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa dakarun da mayakan ta'addancin sun yi musayar wuta a daren Laraba, 13 ga watan Mayu.

Sagir Musa, kakakin rundunar sojin a wata takarda da ya fitar, ya ce sun yi nasarar kwace wasu motocin yaki daga 'yan ta'addan.

Sai dai cike da alhini, ya sanar da cewa dakarun Najeriya biyu sun samu kananan raunika.

"Dakarun sashi na farko na Operation Lafiya Dole sun yi nasarar mayar da martanin harin da mayakan ta'addanci suka kai musu a ranar Laraba.

"Yan ta'addan sun kai wa sojojin hari ne a yankin Mainok zuwa Jakana da ka karamar hukumar Kaga ta jihar Borno.

"Maharan sun iso ne wurin karfe 6 da rabi na yammacin ranar Laraba," takardar tace.

"Sojojin sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda tara, sun kwace motocin yakin su biyu da kuma wasu bindigogi. Sojoji biyu ne suka samu kananan raunika.

"A halin yanzu, komai ya koma daidai a yankin," ya kara da cewa.

A makon da ya gabata ne dakarun sojin Najeriya suka dinga kai wa 'yan ta'addan hari babu kakkautawa.

Adadin 'yan ta'addan da dakarun Najeriya suka halaka a daren jiya - Rundunar soji
Adadin 'yan ta'addan da dakarun Najeriya suka halaka a daren jiya - Rundunar soji. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: A karo na biyu: Ganduje ya bada tallafi don rage wa jama'ar Kano radadi

A wani labari na daban, shugaban dakarun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, ya bayyana cewa rundunar sojin saman Najeriya za ta kara yawan dakarunta a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Kamar yadda shugaban ya bayyana, rundunar za ta yi hakan ne don kokarin ganin karashen halaka Boko Haram a yankin.

Ya bada wannan tabbacin ne a jiya, yayin ziyarar da ya kai ta kaddamar da wasu ayyuka a hedkwatar sojin saman ta rundunar Operation Lafiya Dola a Maiduguri.

Ya jinjina wa kokarin rundunar na kammala ayyuka 889 a cikin wata ukun farko na shekarar nan wanda suka yi shi don murkushe ragowar 'yan ta'addan.

"Matasalar tsaro babban kalubale ne ga ci gaban mu. Dole ne mu tabbatar da kawo karshen sa. Ina farin cikin ganin ci gaban da ake samu yayin yaki da 'yan ta'addan.

"Na yi farin cikin ganin yadda sojin saman suka yi aiki a sama na sa'o'i 1690, ayyuka 889 da kuma tarwatsa mafakar 'yan ta'adda 33 a cikin watanni uku na farkon 2020.

"Rundunar sojin saman za ta ci gaba da kokari. Wasu daga cikin abubuwan da za mu kaddamar sun hada da karin ma'aikata don karasa 'yan ta'addan da suka rage," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel