Bayan musanta wa, gwamnatin Yobe ta tabbatar da mutuwar mutum 471

Bayan musanta wa, gwamnatin Yobe ta tabbatar da mutuwar mutum 471

Bayan makonni da gwamnatin jihar Yobe ta dauka tana musanta wa, daga bisani ta amince cewa an rasa rayuka 471 a cikin makonni uku a jihar.

A wasu jerin rahotanni, an ji yadda mutanen jihar ballantana tsofaffi suka dinga mutuwa bayan sun bayyana da wasu alamun cutar korona, lamarin da ya firgita zukatan jama'ar jihar.

Lamarin ya kai har makabartu sun fara cika a jihar.

Amma kuma duk da musantawar da gwamnatin jihar ta yi, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya nuna damuwarsa a kan mace-macen da ke aukuwa. Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta fara bincike a kan lamarin.

Bayan jin wannan shawarar, gwamnatin jihar Yobe ta gano cewa mace-macen da ake yi a jihar gaskiya ne.

A yayin tabbatar da al'amarin a ranar Talata, kwamishinan lafiya na jihar, Dr Muhammad Lawan Gana, wanda shine mataimakin shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar, ya ce mutanen da suka rasa rayukansu yawanci tsofaffi ne.

Bayan musanta wa, gwamnatin Yobe ta tabbatar da mutuwar mutum 471
Bayan musanta wa, gwamnatin Yobe ta tabbatar da mutuwar mutum 471. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Atiku da Saraki sun yi martani a kan nadin Farfesa Gambari

Ya kara da cewa mutum 471 sun rasu tsakanin satin karshen wata Afirilu da kuma mako na biyu na watan Mayu.

Kamar yadda Gana ya bayyana, sama da kashi 57 na mamatan tsofaffi ne, kuma kashi 58.5 duk maza ne.

Ya ce an samu mace-macen ne a karamar hukumar Potiskum, Nguru, Gashua da babban birnin jihar na Damaturu.

Gana ya ce, "kashi 57 daga cikin mamatan na da wasu ciwukan wadanda suka hada da hauhawar jini, ciwon sukari, ciwon koda ko kuma hatsari ya kawo mutuwar su.

"16 daga ciki ne 'yan uwansu suka bayyana cewa alamun ciwo daya ya kashe su. Bayan bincike an gano cewa COVID-19 ne ciwon da ya kashe 16 daga ciki."

A wani labari na daban, cutar korona ta kashe Dr Kabir Tijjani, shugaban babban asibitin Mani da ke jihar Katsina.

Babban likitan ya rasu ne a ranar Talata kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta sanar wa SaharaReporters.

Majiyar ta ce an gano marigayin na dauke da muguwar cutar ne a makon da ya gabata kuma an mayar da shi daya daga cikin cibiyoyin killacewar da ke jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel