Atiku da Saraki sun yi martani a kan nadin Farfesa Gambari
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Dr. Bukola Saraki sun mika sakon taya murnarsu ga Farfesa Ibrahim Agboola Gambari.
Sun taya shi murnar sabon mukamin da aka nada shi a yau na shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Atiku ya mika sakon taya murnar ne ta shafinsa na Twitter. Ya ce, "Ina taya Farfesa Ibrahim Agboola Gambari murna da nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa."
"Muna fatan zai cimma tsammanin 'yan Najeriya da shekaru tare da gogewarsa a ayyuuka daban-daban da ya yi," dan takarar kujerar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a 2019 ya wallafa.
Saraki ya kwatanta Gambari da mutum mai natsuwa, mai tarin ilimi kuma gogaggen dan difulomasiyya.
Ya kara da cewa sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar "yana tafe da duk abinda ake bukata don yin aikinsa yadda ya dace."
"Bani da tantama zai yi fiye da abinda ake tsammani. Ina kira ga 'yan Najeriya da su ba shi goyon baya ta yadda zai sauke nauyin da aka dora masa", cewar Saraki.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Abinda yasa na daina sumbata da rungumar mata a fim - Ali Nuhu
A jiya ne Legit.ng ta wallafa cewa, tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama magajin marigayi Abba Kyari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren majalisar dinkin duniyan a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.
Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma ya yi tsohon ministan harkokin waje tsakanin 1984 zuwa 1985. Farfesan na da babbar shaidar kwarewa da jajircewa.
Yana da shekaru 78 a duniya a yanzu da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari.
Farfesa Gambari ya yi aiki tukuru a yayin da yake sakataren majalisar dinkin duniya, kuma mai bada shawara na musamman ga babban sakataren nahiyar Afrika tsakanin 1999 zuwa 2005.
Mutum ne sananne a gida da wajen kasar nan. Shine shugaban majalisar zartarwa ta jami'ar jihar Kwara a halin yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng