Gwamnatin jahar Yobe ta bayyana abin da ya kashe mutane 471 a jahar

Gwamnatin jahar Yobe ta bayyana abin da ya kashe mutane 471 a jahar

Gwamnatin jahar Yobe ta yi bayani dalla dalla ga al’ummar jahar game da mace macen da aka samu a jahar a yan kwanakin nan wanda ya tayar da hankulan al’ummar jahar.

Kwamitin kar-ta kwana dake yaki da annobar Coronavirus na jahar Yobe ne ta bayyana haka yayin taron gabatar da jawabi da ta gudanar a garin Damaturu a ranar Talata, 12 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m

Shugaban Kwamitin, mataimakin gwamnan jahar, Idi Garba Gubana ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna an samu mutuwar mutane 471 zuwa ranar Litinin, a jahar Yobe.

Kashi 57 daga cikinsu na fama da cututtuka daban daban da suka dade suna damunsu, amma babu wani hujja daya nuna wuri guda da aka samu mace mace da dama.

Gwamnatin jahar Yobe ta bayyana abin da ya kashe mutane 471 a jahar
Gwamnatin jahar Yobe ta bayyana abin da ya kashe mutane 471 a jahar Hoto: Shafin Usman Ibrahim Geidam
Asali: Facebook

Hakazalika binciken ya tabbatar da kashi 96 na mamatan suna da tarihin yin tafiye tafiye zuwa wajen jahar Yobe, amma kashi 90 daga cikinsu basu dauke da alamun cutar COVID-19.

Bugu da kari kashi 58.7 na mamatan maza ne, amma mutane 16 daga cikin yan uwan mamata 471 sun nuna wasu alamun cututtuka da yan uwansu da suka mutu suka nuna kafin su mutu.

Dukkanin mutanen 16 an gudanar da bincike a kansu, kuma an mika su zuwa asibiti, 3 daga cikinsu sun nuna alamun cutar Coronvirus, kuma duka su ukun yan garin Potiskum ne.

A yanzu haka an musu gwaji ana jiran fitowan sakamakon gwajin, don haka an killace su. Daga cikin mamatan kashi 97 yan kasuwa da masu sana’ar hannu ne, kashi 3 ma’aikatan gwamnati.

Idan za’a tuna, Allah ya yi wa wani hamshakin dan kasuwa mai suna Abdullahi Nuhu rasuwa a jahar Yobe. Ya rasu bayan ya bayyana da wasu alamun cutar COVID-19 a tattare da shi.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Zamfara ta sanar da mutuwar manyan sakatarorinta guda biyu a cikin kwanaki biyu sakamakon wata yar gajeruwar rashin lafiya da suka yi fama da ita.

Jaridar Punch ta ruwaito manyan jami’an gwamnatin da suka mutu sun hada da Alhaji Yawale Dango, babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan jahar.

Sai kuma Alhaji Ahmed Sale, babbana sakatare a ma’aikatan gidaje da cigaban biranen jahar Zamfara. Sale ya rasu a ranar Talata, yayin da Dango ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel