An rasa rayuka 6 bayan musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun soji

An rasa rayuka 6 bayan musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun soji

A kalla rayuka shida aka rasa bayan ruwan wutar da ya wanzu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a wani kauyen da ke jihar Binuwai.

'Yan bindigar sun kai hari kauyen a daren Litinin da ke yankin Agasha ta karamar hukumar Guma da ke jihar.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa maharan sun shiga kauyukan da karfe 11:30 na dare inda suka fara harbe-harbe. Sun kashe mutum 2 tare da raunata wasu daban.

Ganau ba jiyau ba sun sanar da gidan talabijin din Channels cewa, an harbi wata tsohuwa da ke zama a kusa da makarantar firamare ta Agasha yayin harin.

Kwamandan Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya sanar da manema labarai a garin Makurdi cewa: "wasu 'yan bindiga sun shiga garin Agasha da ke karamar Guma na jihar Binuwai inda suka kashe mazauna kauyen biyu.

An rasa rayuka 6 bayan musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun soji
An rasa rayuka 6 bayan musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun soji. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

"Rundunar Operation Whirl Stroke da ke sintiri a yankin sun hanzarta zuwa wurin amma sai 'yan bindigar suka tsere.

"Dakarun sun hanzarta bin 'yan bindigar cikin daren yayin da dakarun da ke Tomatar suka rufe hanyar shiga Nasarawa.

"Sai wurin karfe 6 na safiyar Talata ne dakarun suka yi gaba da gaba da 'yan bindigar. A nan ne aka halaka hudu daga cikin 'yan bindigar tare da kwace bindigogi biyu, harsasai hudu da sauransu."

Yekini ya kara da cewa babu wanda aka kashe a cikin dakarun. Ya jaddada cewa dakarun a halin yanzu suna ci gaba da binciko 'yan ta'addan a yankin.

A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda sun ceto wasu mata biyu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace su a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Ya yi bayanin cewa sun yi nasarar ceto matan bayan kiran da suka samu a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

'Yan bindigan da za su kai 10 sun tsinkayi kauyen Sabon Layi a babura dauke da bindigogi kirar AK 47 inda suka yi awon gaba da matan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel