Abubuwa 13 game da Ghebreyesus, mutumin dake yaki da Coronavirus a duniya gaba daya

Abubuwa 13 game da Ghebreyesus, mutumin dake yaki da Coronavirus a duniya gaba daya

Tun bayan bullar annobar Coronavirus a duniya ake ta jin sunan wani mutumi, Tedros Adhanom Ghebreyesus a kafafen watsa labaru da dandalin sadarwar zamani.

Mista Ghebreyesus ne babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, don haka ya zamto jagorar yaki da duk wasu cututtuka a duniya tare da tabbatar da ingancin lafiyan jama’a.

KU KARANTA: Yaki da Coronavirus: Ganduje ya kaddamar da rabon takunkumin fuska miliyan 2

Abubuwa 13 game da Ghebreyesus, mutumin dake yaki da Coronavirus a duniya gaba daya
Ghebreyesus, mutumin dake yaki da Coronavirus a duniya gaba daya Hoto:WHO
Asali: UGC

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman bayanai 13 game da Ghebreyesus:

- Tedros Adhanom Ghebreyesus dan asalin kasar Ethopia ne a nahiyar Afirka

- An haife shi a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1965, shekarunsa 55

- A shekarar 2017 ya zama shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO

- Kwararren mai bincike ne a fannin cutar zazzabin cizon sauro

- Shi ne dan Afirka na farko da ya fara rike wannan muhimmin mukami

- Shi ne mutum na farko daya fara rike wannan mukami wanda ba likita ba

- Ya taba zama ministan kiwon lafiya a Ethiopia 2005-2012

- A ministan kiwon lafiya ya gina cibiyoyin kiwon lafiya 4,000

- Ya taba zama ministan harkokin kasashen waje 2012 -2016

- Ya yi karatun digiri a fannin Biology a shekarar 1986 a jami’ar Asmara

- Ya yi digiri na biyu a jami’ar tsaftar muhalli ta Landan a fannin Immunology of Infectious Diseases

- Ya yi digirgire a jami’ar Nottingham a fannin kiwon lafiyar al’umma.

- Tedros na da mata da yara 5

A wani labari kuma, gwamnatin tarayyar Najeriya ta zabi Legas, Abuja, Ogun, Kaduna, Sokoto da Kano a matsayin inda WHO za ta yi gwajin maganin cutar Coronavirus.

Gwajin wanda gwajin ingancin maganin ne na duniya na daga cikin kokarin hukumar kiwon lafiyan na samar da magani da kuma riga-kafin korona a cikin kankanin lokaci.

Ayanzu haka cutar Coronavirus ta kama mutane fiye da miliyan 4 a duniya, ta kashe mutane 285,000 yayin da mutane miliyan 1.4 suka warke daga cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel