COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya

COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da gwada maganin korona na WHO a kan jama'ar jihohi shida a Najeriya

- Kamar yadda ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ya sanar, za a gwada maganin a kan jihohin Legas, Ogun, Abuja, Kaduna, Sokoto da Kano

- A bangaren jihohin Cross River da Kogi da ba a samu mai cutar ba, kwararru daga ma'aikatar lafiya za su garzaya birnin Calabar don tallafi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce jihohin Legas, Abuja, Ogun, Kaduna, Sokoto da Kano ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya za ta gwada maganin cutar korona a kan mutanen ta, SaharaReporters ta wallafa.

Gwajin maganin, wanda gwajin ingancin maganin ne na duniya na daga cikin kokarin kungiyar kiwon lafiyan na samar da magani da kuma riga-kafin korona a cikin kankanin lokaci.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Abuja yayin jawabi a kan inda kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona suka kwana.

Ehanire ya ce zuwa ranar Lahadi, kasar nan ta kara gwajin samfur 1,127 inda jimillar gwajin da aka yi ya kai 27,078. 4,399 daga ciki kuwa duk suna dauke da cutar daga jihohi 35 na kasar nan. Kashi 70 bisa dari duk maza ne.

COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya
COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Aso Villa: Wata sabuwar guguwa na kokarin yi wa 'Cabals' juyin mulki

Ya ce, "Gwamnatin tarayya na bai wa WHO hadin kai don gwajin maganin korona a jihohin Legas, FCT, Ogun, Kaduna, Sokoto da Kano.

"Har zuwa ranar Litinin, Najeriya ta gwada karin mutum 1,127 wanda hakan ya kai jimillar gwajin zuwa 27,078 da aka yi a fadin kasar nan.

"Mutum 4,399 daga jihohi 35 duk suna dauke da kwayar cutar yayin da maza ke da kaso 70 cikin 100 na masu cutar.

"Jihohin Kogi da Cross River har yanzu basu da mai cutar. Amma za mu yi aiki da karamin ministan lafiya na kasa don duba jihar da kyau.

"Kungiyar kwararru daga ma'aikatar lafiya za su garzaya Calabar bayan sun kammala shirye-shirye don bada tallafi ga cibiyoyin lafiyarsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel