COVID-19: NCDC ta yi martani a kan 'korar kare' da gwamnan Kogi ya yi musu

COVID-19: NCDC ta yi martani a kan 'korar kare' da gwamnan Kogi ya yi musu

Darakta janar din hukumar kula da yaduwar cututtuka masu yaduwa (NCDC), ta ce jihar Kogi ta kore su a kokarinsu na bada taimako wajen tabbatar da halin da jihar ke ciki a kan annobar COVID-19.

Jihohin Kogi da Cross River ne jihohi biyu a Najeriya wadanda har yau ba a samu ko mutum daya da ke dauke da cutar ba a kasar nan.

Gwamnatin jihar Kogi ta zargi cewa ana kokarin tilasta ta a kan ta bayyana cewa akwai cutar a jihar, kamara yadda jaridar The Cable ta wallafa.

A yayin da wakilai daga NCDC suka ziyarci jihar a ranar Talata da dare, Gwamna Yahaya Bello ya bukaci kungiyar jami'an da su killace kansu na kwanaki 14 ko kuma su bar jihar a take.

Wannan lamarin ne yasa kungiyar jami'an suka tattara zuwa babban birnin tarayya na Abuja.

A yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar COVID-19 na kasa a ranar Juma'a, shugaban NCDC ya ce za su iya taimako ne matukar ana bukatar hakan.

COVID-19: NCDC ta yi martani a kan 'korar kare' da gwamnan Kogi ya yi musu
COVID-19: NCDC ta yi martani a kan 'korar kare' da gwamnan Kogi ya yi musu. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

"Taimakonmu zai iya amfani ne a inda ake bukata. A ranar Talata, mun so bada taimako amma ba a bukata. Abin takaici da alhini ne ya faru a ranar," Ihekweazu yace.

Kamar yadda ya kara da cewa, "Mun tallafawa Kogi ta duk inda ya kamata, jihar ce ke da cibiyar gaggawa ta farko da NCDC ta fara bai wa tallafi.

"A takaice, amfaninmu shine tallafa wa jihohi. Babban aikinmu shine tabbatar da tsaro ta fannin cibiyoyin lafiya. Muna tallafi kuma da gaske muke yi."

A yayin jawabin Bello bayan karbar tawagar gwamnatin tarayyar, ya bayyana mayakan da jihar ta dauka wajen yaki da annobar.

Ya ce jihar na da matukar gogewa wajen yaki da cututtuka masu yaduwa wadanda suka hada da zazzabin Lassa da na Malaria.

Ya ce wadannan gogewar ne ake amfani da su a wannan halin. Ya bukaci jami'an NCDC da a gwada su tare da killacesu a cibiyar killacewa ta jihar ko kuma su kama gabansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel