Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

- Kamar yadda jaridar HumAngle ta wallafa, rahoton da ke yawo na cewa Abubakar Shekau ya samu tallafi daga wata kungiya duk bogi ne

- Rahoton na bayyana cewa wata kungiya ta bai wa Abubakar Shekau tallafin Euro miliyan 5 wanda ya jawo tashin hankali a sansanin

- Kudin yasa ba a ganin Abubakar Shekau banda hadimansa na kusa da shi don bai yadda a raba kudin ba

Kamar yadda jaridar HumAngle ta wallafa, ta kwatanta rahoton da ke yawo a yanar gizo a kan sashen Abubakar Shekau na Boko Haram duk na bogi.

Rahoton na bayyana cewa Shekau da mutanensa sun hargitse bayan wata kungiyar taimakon kai da kai ta basu tallafin kudin har Euro miliyan biyar.

Labarin ya yi ikirarin cewa wata majiya ta rundunar sojin ta ce, "Idon Shekau ya rufe a yanzu don sai hadimansa na kusa ke iya samunsa. Tallafin kudin da suka samu yana neman hargitsa sansanin.

"Tun a baya Shekau ya saba samun tallafin kudi amma bai taba kawo sauye-sauye a fannin ababen more rayuwa a sansanin. Kwamandojinmu basu damu da cewa yana damfarar mu bane.

"Idan akwai abinda muke so yanzu, bai wuce a kama shi ba don kada mayakansa su halaka shi," majiya daga rundunar sojin Najeriya ta bayyana kamar yadda suka yi ikirari.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa

Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana
Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Amma kuma kamar yadda jaridar HumAngle ta bayyana, daraktan hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya, Sagir Musa, ya ce bai san wannan labarin ba kuma bashi da tabbacin ikirarin cewa wata kungiya ta tallafa wa Shekau da kudi.

Jaridar ta ce ta duba inda aka dangana da samo labarin amma babu labarin ko alamarsa.

Hakazalika, babu wata alama da ke nuna cewa ana barin wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na aiki a yankin.

Wannan ya biyo bayan ganowa da aka yi cewa Shekau na samu tallafin kudi a baya daga wurarensu.

Kamar yadda jaridar HumAngle ta gano, Abubakar Shekau ba ya dogara da tsarin Shura.

Rahoto ya bayyana cewa Abubakar Shekau ba ya sassauta wa kungiyoyin adawa,, lamarin da yasa sauran kwamandojin Boko Haram basu taba sukar ra'ayinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel