Cibiyoyin kula da masu Coronavirus sun gamu da wata babbar kalubale – Boss Mustapha
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa cibiyoyin kula da masu cutar Coronavirus a duk fadin kasar na fama da wata babbar matsala ta rashin gadajen kwantar da marasa lafiyan.
Punch ta ruwaito sakataren gwamnatin tarayya, kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana ta shugaban kasa dake yaki da cutar, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.
KU KARANTA: An samu bullar annobar COVID-19 a yankunan karkara – Gwamna El-Rufai
Mustapha ya bayyana haka ne yayin da kwamitin ke yi ma yan Najeriya jawabi game da halin da ake ciki na Coronavirus a kasar.
A jawabinsa, Mustapha yace sun zage damtse a kan sa ido game da bin dokoki da umarnin gwamnatin tarayya dangane da abin janye dokar ta baci da ta yi a duk fadin kasar.

Asali: UGC
Boss yace kwamitin ta gana da shuwagabannin hukumomin tsaro inda ta nemi su dabbaka umarnin shugaban kasa na hana tafiye tafiyen jama’a tsakanin jahohi don rage yaduwar cutar.
“Binciken da muka yi ya nuna har yanzu jama’a na karya dokokin da aka sanya, kuma hakan mummunar manuniya ce ga hadarin da ka iyo biyo baya. A yanzu haka mun kai matakin da cutar na yawo a cikin al’ummarmu.
“Kuma a jiya Alhamis, 7 ga watan Mayu mun samu adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar a ranar daya, 381. Wannan abin damuwa ne, sai dai kuma ana samu yawan jama’an ne saboda mun kara yawan cibiyoyin gwaje gwajen mu wanda ya bamu daman gano masu cutar.
“Sai dai yawan mutanen dake da cutar ba yana nufin yawan mace mace daga cutar bane, kuma ana cigaba da samun mutane da dama da suke warkewa daga cutar. Haka zalika mun samu rahotanni daga jahohi cewa cibiyoyin kula da masu cutar suna fama da matsalar rashin gado.
“Za mu cigaba da kula da irin yanayin mu, tare da kawo sauye sauye ga hanyoyin da ake bi wajen kula da masu cutar, sai kuma mu duba wasu zabi na daban, zamu sanar da wadannan sauye sauyen nan bada jimawa ba.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng