Tsakanin zuwa Masallaci da Kasuwa lokacin Korona: Menene ya dace da ka'idojin manufar Musulunci - Sheikh Dogarawa
Rubutun Sheikh Ahmad Bello Dogarawa
Kiraye-kiraye sun fara yawa game da bukatar a janye dokar dākatar da sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i saboda ba da dama da gwamnatoci suka yi ga mutane su fita a cikin wasu ranaku don zuwa kasuwa.
Akwai wadanda ke cewa an rufe masallatai amma an ba mutane damar su je kasuwanni da banki da wuraren neman abinci saboda sallar ce kawai ba a so a yi a cikin masallatai.
Haka kuma, wasu su na zuwa filin kwallo da wuraren shakatawa amma gwamnatoci ba su hana ba. Masallaci kuwa an ce kar a je, saboda an raina Musulunci da Musulmai.
Tambaya ita ce: mene ne ya dace da tabbatattun kā’idodi da manufofin Sharī’ar Musulunci?
Abin da ya kamata gwamnatoci su yi shi ne rufe kasuwanni da dukkan wuraren da mutane ke taruwa, kamar yadda aka dākatar da sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i a masallaci na wacin gadi don ganin an dākile yāduwar annobar korona.
Wannan ita ce shawarar masana fannin kiwon lafiya.
Toh amma akwai bukatar a fahimci abubuwa kamar haka:
1. Idan gwamnati ba za ta iya hana zuwa kasuwa ba saboda ba ta yi wa mutane tanadin abin da za su ci ba, kuma ya zamanto barin mutane su taru a masallatai da kuma kasuwa zai sakwarkwatar da dokar zaman gida, idan ya zama dole a dauki daya a bar daya, kasuwa ce za a bar mutane su je, ba masallaci ba, saboda:
(i) Fita neman abinci hanya (وسيلة) ce ta tabbatar da ba da kāriya ga rayuwa, amma zuwa masallaci don yin sallar jam’i cikasawa (مكمل) ce ga wasīlar da ke tabbatar da ba da kāriya ga addini;
(ii) a babin rangwame na Sharī’ah saboda uzuri ko larura, hakkin Allah ne ya fi saukin a jingine na wacin gadi fiye da hakkin bayin Allah, domin kamar yadda Mālamai suka bayyana, hakkokin Allah sun ginu ne a kan kyauta da rangwame (مسامحة), a yayin da aka gina hakkokin bayin Allah a kan rowa da rashin rangwame (مشاحة);
(iii) sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i na da makwafi idan ba a samu yin su ba, amma fita neman abinci ko zuwa wajen harkokin saye da sayarwa ba shi da makwafi idan gwamnati ba ta samar wa mutane abin da za su ci ba idan sun zauna gida.
(2) Ko da yake wasu Mālamai na ganin cewa ana gabatar da hakkin kiyaye addini (حفظ الدين) a kan hakkin kiyaye rai (حفظ النفس), Mālamai irin su Ar-Rāziy, da Al-Qarrāfiy, da Al-Baidāwiy, da Ibn Taimiyyah, da Al-Isnawiy, da Az-Zarkashiy sun rinjayar da wajabcin ba da kāriya ga rai a kan ba da kāriya ga addini, kasancewar kiyaye addini ba ya yiwuwa ba tare da an kiyaye rayukan wadanda za su yi addini ba.
Sun dogara da ayar, “Sai dai wanda aka tursasa shi (ya fadi kalmar kafirci) alhali zuciyarsa na cike da imani” [Nahl, 106].
A karkashin wannan asali ne, Malamai suka yi bayani game da dauke sallar Jumu’ah ko sallar farilla cikin jam’i saboda tsoron tozartar dukiya ko saboda jinyar mara lafiya ko jiran gawa idan ana tsoron ka da ta tozarta idan aka bar ta.
Bisa wannan dalili, idan ya zamanto akwai larurar ko dai a bar mutane su fita zuwa neman abin da za su ci ko kuma a bar su fita zuwa masallaci don sallar Jumu’ah da sallolin farilla cikin jam’i, toh, za a gabatar da barin mutane su je kasuwa a kan barin su su je masallaci.
(3) Adadin masu zuwa masallaci ya ninninka adadin masu zuwa kasuwa kasancewar mutane da yawa ba sa zuwa kasuwa amma suna zuwa masallaci.
Sannan, hadarin cudanyar da a ke yi a masallaci saboda hada sahun salla ya fi hadarin cudanyar da a ke yi a kasuwa kasancewar mutane na da damar tsayawa nesa da juna a yayin saye da sayarwa.
(4) Idan mutane suka ki bin umarnin gwamnati game da zaman gida bisa hujjar cewa sai sun fita za su samu abinci, wannan ba zai zama uzuri ga mutane su sāba wa dokar dākatar da yin salloli a masallaci ba.
(5) Ba daidai ba ne daidaikun Malamai ko dāliban ilmi ko shugabannin kungiyoyin addini su yi kira ga hukumomi a kan su ba da damar a cigaba da sallar Jumu’ah ba.
Wannan zai kawo rashin tsari da kuma rudani a cikin al’umma, musamman da yake wannan mas’ala ce da ta shafi makomar al’umma gaba daya.
Kamata ya yi Malamai da dāliban ilmi su tuntubi juna don su dauki matsaya guda daya bayan sun tattauna da amintattun, nagartattun kwararrun masana harkokin kiwon lafiya da ilmin cututtuka don sanin halin da a ke ciki game da annobar da kuma ko lokaci ya yi na janye dokar.
Daga karshe, ina rokon Allah Ya yaye mana wannan annoba kuma Ya ba mu mafita daga abubuwan da suka addabe mu.
Wallahu A’alam.
Asali: Legit.ng