Ku gafarce ni, aikin shaidan ne: Faston da ya lalata kananan yara hudu ya nemi gafara

Ku gafarce ni, aikin shaidan ne: Faston da ya lalata kananan yara hudu ya nemi gafara

Jami'an tsaro a Benin City sun damke wani fasto da ya lalata yara hudu masu shekaru daga shida zuwa goma sha daya, uku daga ciki 'yan uwan juna ne.

Babbar cikin kananan yaran 'yan uwan juna na da shekaru tara, yayin da karamar ke da shekaru shida.

Fasto Otobong Emerson mai shekaru 48 na babbar cocin Believers Ministry na zaune a gida mai lamba 146 da ke titin Owina kusa da Evbuotubu a garin Benin City.

Yana daga cikin wadanda ake zargi da jami'an 'yan sanda suka damke a jihar Benin a ranar Juma'a.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, faston ya yi lalata da yaran babu adadi kuma ya amsa laifinsa saboda rashin kwanciyar hankali da ya shiga.

"Bayan lalata da yaran sau babu adadi, alhakinsu ya fara bi na don haka naje na sanarwa da babban fasto na. Ban san abinda ya kaini ba amma na yi nadama," yace.

Ku gafarce ni, aikin shaidan ne: Faston da ya lalata kananan yara hudu ya nemi gafara
Ku gafarce ni, aikin shaidan ne: Faston da ya lalata kananan yara hudu ya nemi gafara. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kanin Malam Mamman Daura rasuwa

Ya dangana mummunar aika-aikarsa da sharrin shaidan tare da neman yafiya da gafara.

Hukumar 'yan sanda sun fara bincikarsa kuma ya amsa laifinsa, DSP Chid Nwabuzor ya sanar.

"An mika al'amarin zuwa kotu kuma wanda ake zargin yana garkame a hannun 'yan sanda.

"Zai bayyana a gaban kotu a ranar 11 ga watan Yunin 2020," yace.

'Yan sandan sun kama wani mutum mai suna Joshua Aiworo mai shekaru 38 da matarsa mai suna Blessing Ogieva mai shekaru 25.

Ana zarginsu da laifin siyar da jaririn watanni biyu ga wata mata mai suna Felicia Imaguomaruomwan a kan N300,000.

Nwanbuzor ya ce 'yan sandan sun samo jaririn kuma daga baya sun mika shi gidan marayi da ke Oka, titin Upper Sakponba a garin Benin City don samun kula.

Ba wannan bane karo na farko da aka fara samun masu safarar jarirai ko kananan yara ba. Su kan siyar da su ga jama'ar da basu sani ba a kananan kudi don samun biyan bukatarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel