An bayyana dalilin da ya sa Buhari ya yi burus da bukatar Ganduje ta neman biliyan N15 don yakar korona a Kano
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilan da suka sa shugaba Buhari ya ki amsa bukatar gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta bawa gwamnatinsa biliyan N15 domin yakar annobar korona da ta bulla a jihar, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.
A cikin watan Maris ne shugaba Buhari ya amince da bawa jihar Legas biliyan N10 da bawa jihar Ogun biliyan N5 a matsayin tallafin yaki da annobar korona.
Kwanaki kadan bayan bullar annobar korona a Kano, gwamna Ganduje ya nemi tallafin biliyan N15 daga gwamnatin tarayya domin dakile yaduwar annobar a jihar Kano.
Daily Nigerian ta wallafa rahoto a kan yadda bukatar ta Ganduje ta jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya a wancan lokacin.
A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin gidan radiyon Wazobia FM mai taken 'As E Dey Hot', kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari ya yi burus da bukatar duk gwamnonin da suka nuna fifiko a kan kudi bayan bullar korona a jihohinsu.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar bawa Lagos da Ogun tallafin kudi bayan ta gamsu cewa jihohin suna da shiri da tsare - tsaren yaki da annobar da ta bulla jihohinsu.

Asali: Depositphotos
Ya kara da cewa jihar Legas ba ta nemi tallafin kudi ba, ta nemi tallafin ma'aikata da kayan aiki ne kawai daga FG.
A cewar Adesina, gwamnatin Buhari ta ga dacewar bawa gwamnatin Legas kudin ne ba don ta nema ba, sai don ta gamsu cewa ya kamata ta yi hakan.
DUBA WANNAN: An sallami Farfesa Habeeb, kwamishinan lafiya da sauran mutane 14 da suka warke daga korona a Kano
Adesina ya kara da cewa duk gwamnonin da suka nemi tallafin kudi kai tsaye daga bullar annobar a jihohinsu, ba lallai su samu ba.
"Sun ce ko kwana 30 ba a yi ba Legas ta samu tallafin kudi, aiyukan da gwamnatin tarayya ta ga jihar na yi ne suka sa ta taimaka mata da biliyan N10.
"Duk wata jiha da ke yin kokarinta ba tare da yin gunaguni da korafin 'a bamu kudi, a bamu kudi ba', gwamnatin tarayya za ta bata duk gudunmawar da ta dace, kamar yadda ta bawa Legas tallafin kudi.
"Tanadi da tsare - tsare a matakin jiha suna da matukar muhimmanci, kokarin da Legas ta yi a wannan bangare ne yasa ta samu tallafin kudi.
"Shi yasa shugaban kasa shugaban kasa ya tura tallafin muhimman aiyuka zuwa Kano, wanda hakan shine abinda gwamnati ta ga ya fi dacewa a lokacin," a kalaman Adesina, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng