Boko Haram: Yadda 'yan ta'adda suka fi karfin 'yan sa kai, sun yi barna a Borno

Boko Haram: Yadda 'yan ta'adda suka fi karfin 'yan sa kai, sun yi barna a Borno

Wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari yankin Deboro da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Wadanda ake zargin sun tsinkayi yankin a ranar Laraba a motoci biyar kirar Hilux inda suka fara harbe-harbe, lamarin da yasa mazauna yankin suka tsere zuwa daji.

Mayakan ta'addancin sun firgita mazauna kauyen don sun kasa mayar da martani sakamakon rashin 'yan sanda ko sojoji a kusa da kauyen.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana, 'yan sa kai da suka yi yunkurin mayar musu da martani an fi karfinsu don haka suka tsere tare da barin 'yan ta'addan suna cin karensu ba babbaka.

Wasu daga cikin mazauna yankin da suka zanta da gidan talabijin ta waya, sun tabbatar da cewa har yanzu suna maboyarsu don babu tabbacin cewa 'yan bindigar sun tafi.

Makarantar firamare da sauran gine-ginen gwamnati duk 'yan bindigar sun kone su.

Har yanzu ba a tabbatar da cewa an rasa rayuka ba don bayanai a kan harin basu da yawa.

Debiro gari ne da ke da nisan kilomita 48 daga karamar hukumar a Biu.

An fara kai musu hari a shekarar 2018.

Boko Haram: Yadda 'yan ta'adda suka fi karfin 'yan sa kai, sun yi barna a Borno

Boko Haram: Yadda 'yan ta'adda suka fi karfin 'yan sa kai, sun yi barna a Borno. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC

A wani labari na daban, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a jiya Laraba ya ce barazanar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa maso yamma da jihar Katsina ya sa jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati.

A yayin zantawa da shugaban horarwa, Janar Leo Irabor wanda ya kai masa ziyara, ya ce mazauna jihar sun fara kokarin tunkarar 'yan bindigar don hare-haren kullum kara yawaita suke.

"A halin yanzu ina cikin rudani. Ina da kayyadaddun kayan aiki da jami'ai. A tunanina idan aka karfafa jihar nan da kayan aiki da ma'aikata, za mu ga karshen wannan jarabawar," yace.

"Halin da yankin Arewa maso yamma ke ciki abin tashin hankali ne. Annobar Coronavirus ce ke rufe labaran kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a yankunan. A koda yaushe muna cikin barazana ne," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel