COVID-19: Darakta a ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe ya rasu a cibiyar killacewa

COVID-19: Darakta a ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe ya rasu a cibiyar killacewa

- Alhaji Muazu Brahji, darakta a ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe ya rasu yayin da yake cibiyar killacewa ta jihar

- Dan uwan mamacin mai suna Yau Ubaliyo Abubakar ne ya tabbatar da hakan ga wakili Daily Trust a Damaturu

- Jihar Yobe na daga cikin jihohin da basu da dakin gwajin cutar korona a kasar nan, su na kai samfur Abuja ko Borno don gwaji

Darakta a ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe, Alhaji Muazu Brahji ya rasu bayan an kwantar da shi a cibiyar killacewa ta asibitin kwararru da ke Damaturu.

Dan uwan mamacin, Yau Ubaliyo Abubakar ne ya tabbatar da wannan ci gaban ga wakilin jaridar Daily Trust.

Ya bayyana cewa, an kai marigayi Brahji cibiyar killacewar tun a ranar Talata.

Yayin da aka tambayesa ko dan uwansa na dauke da muguwar cutar COVID-19 kafin rasuwarsa, Abubakar ya bayyana cewa an dauka samfur dinsa amma har yanzu sakamakon suke jira.

Jihar Yobe na daga cikin jihohin da basu da dakin gwajin a kasar nan. Samfur din jini idan an diba sai an kaisu Abuja ko jihar Borno don gwaji.

COVID-19: Darakta a ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe ya rasu a cibiyar killacewa
COVID-19: Darakta a ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe ya rasu a cibiyar killacewa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC

A wani labari na daban, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a jiya Laraba ya ce barazanar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa maso yamma da jihar Katsina ya sa jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati.

A yayin zantawa da shugaban horarwa, Janar Leo Irabor wanda ya kai masa ziyara, ya ce mazauna jihar sun fara kokarin tunkarar 'yan bindigar don hare-haren kullum kara yawaita suke.

"A halin yanzu ina cikin rudani. Ina da kayyadaddun kayan aiki da jami'ai. A tunanina idan aka karfafa jihar nan da kayan aiki da ma'aikata, za mu ga karshen wannan jarabawar," yace.

"Halin da yankin Arewa maso yamma ke ciki abin tashin hankali ne. Annobar Coronavirus ce ke rufe labaran kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a yankunan. A koda yaushe muna cikin barazana ne," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel