Yanzu-yanzu: Dan majalisa a jihar Yobe ya kamu da cutar Korona

Yanzu-yanzu: Dan majalisa a jihar Yobe ya kamu da cutar Korona

Dan majalisar jihar Yobe, Lawan Nguru ya kamu da cutar COVID-19, ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Dan majalisar ne ke wakiltar mazabar Nguru kuma shi kadai ne daga jam'iyyar adawa ta PDP a majalisar, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

A wata takarda da ta fito daga dan majalisar a garin Damaturu, ya ce ya killace kansa kamar yadda masana kiwon lafiya suka sanar.

Amma kuma, ya musanta rahoton cewa ya ki killace kansa. Ya jaddada cewa ba zai taba yin zagon kasa ga kokarin gwamnatin jihar na shawo kan annobar tare da saka rayukan jama'a a hatsari ba.

Ya bayyana tabbacin cewa yadda gwamnatin jihar Yobe ke daukar mataki a kan cutar, za a shawo kan annobar.

Ya shawarci jama'ar jihar da su kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiya wajen hana yaduwar cutar.

Nguru ya ce: "A halin yanzu, ina cibiyar killacewa kuma ina samun saukin halin da nake ciki. Ina jiran umarnin likitoci.

"Ina sake jinjina ga gwamnatin jihar Yobe a kan yadda take kula da mu masu jinyar jihar da kuma kokarin hana yaduwar cutar."

Yanzu-yanzu: Dan majalisa a jihar Yobe ya kamu da cutar Korona

Yanzu-yanzu: Dan majalisa a jihar Yobe ya kamu da cutar Korona
Source: Twitter

KU KARANTA: A karon farko: An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta yanar gizo a Najeriya

A wani labari na daban, Wata kotun Najeriya da ke shari'a ta yanar gizo ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yi shari'ar ta yanar gizo ne bayan gwamnati ta rufe kotuna don gudun ci gaban yaduwar annobar korona.

Mutumin mai sun Olalekan Hameed ya samu wannan hukuncin ne a zaman kotun da aka gudanar ta kafar bidiyon a Zoom.

Mai shari'a Mojisola Dada ne ya tabbatar da zartar da hukuncin kisa ta hanyar ratayar a kan Olalekan Hameed. An tabbatar da cewa mai laifin ya kashe mahaifiyar mai gidansa da yake yi wa aikin direba.

A halin yanzu, masu rajin kare hakkin bil Adama sun soki hukuncin. Amma kuma sun yi maraba da sabon salon shari'ar ta yanar gizo saboda annobar korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel