Da duminsa: Korona ta lashe rayuka 93 a Najeriya

Da duminsa: Korona ta lashe rayuka 93 a Najeriya

- Mutum 93 ne suka rasa rayukansa sakamakon annobar Korona a Najeriya

- NCDC ce ta wallafa hakan a shafinta Twitter a ranar Litinin

-A ranar Litinin an samu sabbin mutum 245 masu dauke da muguwar cutar

Mutum 93 ne suka rasu sakamakon annobar Coronavirus a Najeriya.

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

A daren Litinin ne hukumar ta sanar da kara samun sabbin masu cutar har 245 duk da an sallama mutum 417 daga asibiti sakamakon jinya daga cutar.

Duk da dai, gwamnatin tarayya ta dauka alwashin sake rufe wasu sassan kasar nan matukar yawan masu cutar ya ci gaba da karuwa.

Hakazalika, shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar na kasa, Dr Sani Aliyu, ya ce sassauta dokar hana walwalar ba lasisin take dokokin kiwon lafiya bane.

Ya kara da cewa a ci gaba da bin dokokin kiyaye kai daga cutar don gudun komawa gidan jiya.

Da duminsa: Korona ta lashe rayuka 93 a Najeriya

Da duminsa: Korona ta lashe rayuka 93 a Najeriya. Hoto daga NCDC
Source: Twitter

KU KARANTA: Siyasantar da Covid-19: Ganduje ya yi wa shugaban NHIS 'wankin babban bargo'

A wani labari na daban, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mohammed Garba, ya zargi tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf da saka siyasa a yaki da cutar coronavirus.

Shugaban NHIS din ya zargi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dasa cutar a fadin jihohin arewa, jaridar The Nation ta wallafa.

Ya zargi farfesan da kokarin bata wa gwamnan suna tare da tada tarzoma a jihar a maimakon bada gudumawa wurin magance matsalar.

Kwamishinan yada labaran, ya ce cutar ta bulla wasu jihohin arewa tun kafin a sameta a jihar Kano.

Ya jaddada cewa ta isa jihar Kaduna da wasu jihohi hudu ko biyar kafin ta yada zango a jihar Kano. Ta yaya Gwamna Ganduje ya kawo cutar arewa?

Kamar yadda yace, "Kamar yadda farfesan ya bayyana cewa asibitin Malam Aminu Kano bashi da kayan aiki, toh sanannen abu ne idan aka ce asibitin gwamnatin tarayya ne ba na jiha ba.

"NCDC ce ta samar da dakin gwajin don haka babu ruwan gwamnatin jihar da shi."

"Idan za mu tuna, lokacin da aka rufe dakin gwajin na sa'o'i 74, gwamnan ne ya fito ya roki gwamnatin tarayya da ta hanzarta kawo dauki don mutanenshi na cikin damuwa.

"A komai idan aka duba, za mu ga cewa farfesan ne ke siyasantar da al'amura don bata sunan gwamnan.

"Ya yi wallafe-wallafe a kafafen sada zumuntar zamani amma mun kyaleshi. Wannan ce amsa ta farko da ya fara samu," kwamishinan yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel