Ji ka karu: Matakai 6 da ake bukata a dauka ga wanda ya yi mu’amala da mai cutar COVID19

Ji ka karu: Matakai 6 da ake bukata a dauka ga wanda ya yi mu’amala da mai cutar COVID19

Duba da yadda cutar Coronavirus ke yaduwa kamar wutar daji a Najeriya, akwai yiwuwar mutum ya dauka daga wani ba tare da ya sani ba, ko kuma dole ta a yi mu’amala da mai cutar.

Don haka ga wanda ala tilas sai ya yi mu’amala da mai cutar, ko kuma wanda ya yi mu’amala da mai cutar cikin rashin sani, toh ga matakan da ya kamata a dauka don wanyewa lafiya.

KU KARANTA: Kada ka sassauta dokar hana shige da fice sai bayan sati 2 – PDP ga Buhari

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito wasu matakai da hukumar kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya ta nemi jama’a su dauka idan irin haka ya faru;

- Ka sa a ranka cewa lallai wata kila ka kamu da cutar kai ma

- Ka garzaya cibiyar kiwon lafiya sanye da takunkumin rufe fuska

- Ka dauki tazara tsakaninka da mutane, kuma kada ka taba wani wuri da hannunka

Ji ka karu: Matakai 6 da ake bukata a dauka ga wanda ya yi mu’amala da mai cutar COVID19
Takunkumi Hoto:Channels Tv
Asali: UGC

Idan kuma babu cibiyar kiwon lafiya a kusa, ga matakan da suka dace mutum ya dauka kamar haka;

- Mutum ya killace kan sa idan ya fara jin rashin lafiya

- Mutum ya killace kan sa, ya cigaba da lura kan sa tsawon kwanaki 14 idan bai ji rashin lafiya ba

- Idan kuma an tabbatar kana dauke da cutar, ka killace kan ka har sai ka warke

A wani labarin kuma, yan jam’iyyar PDP a majalisar wakilai sun yi kira ga shugaban kasa Buhari ya kara wa’adin dokar ta bacin da ya sanya a Legas, Ogun da Abuja tsawon mako biyu.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ne wa’adin dokar ta bacin da Buhari ya sanya a jahohin uku ya kare, don haka ake sa ran jama’a za su fara fita harkokinsu.

Buhari ya sanya dokar ne don yaki da yaduwar cutar Coronavirus a jahohin duba da cewa su suka fi yawan mutanen da suka kamu da cutar, da kuma wadanda suka mutu daga cutar.

Amma cikin wata sanarwa da yan PDP suka fitar, sun bayyana janye dokar a matsayin abin Allah wadai saboda zai kara ta’azzara yaduwar cutar a tsakanin jama’a fiye da kima.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel