Kada ka sassauta dokar hana shige da fice sai bayan sati 2 – PDP ga Buhari
Ya jam’iyyar PDP a majalisar wakila sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin dokar ta bacin da ya sanya a jahohin Legas, Ogun da Abuja tsawon mako biyu.
Daily Trust ta ruwaito a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ne wa’adin dokar ta bacin da Buhari ya sanya a jahohin uku ya kare, don haka ake sa ran jama’a za su fara fita harkokinsu.
KU KARANTA: Abubuwa 4 da ya kamata masoya su sani game da junansu kafin aure
Buhari ya sanya dokar ne don yaki da yaduwar cutar Coronavirus a jahohin duba da cewa su suka fi yawan mutanen da suka kamu da cutar, da kuma wadanda suka mutu daga cutar.
cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun dan majalisar PDP daga jahar Ribas, Kinsley Chinda, a madadin kafatanin yayan jam’iyyar PDP na majalisar wakilai, sun yi tir da janye dokar.
Sanarwar ta bayyana janye dokar a matsayin abin Allah wadai saboda zai kara ta’azzara yaduwar cutar fiye da kima, don haka ta nemi gwamnati ta raba kayan tallafi ga jahohi.
Haka zalika ta nemi gwamnati ta hada kai da jami’o’i da cibiyoyin bincike wajen lalubo maganin cutar nan mai dauke numfashi, wanda a yanzu ta kashe yan Najeriya 85.

Asali: UGC
“Mun ga halin da ake ciki a Kano da Legas, abin tashin hankali ne, muna la’akari da tabbas shugaban kasa Buhari zai yi sakaci da aikinsa na kare rayukan yan Najeriya kamar yadda ya rantse da kundin tsarin mulkin kasar nan.” Inji ta.
Dan majalisa Chinda ya kara da cewa a makonni 6 da aka dauka ana fama da cutar, gwamnati ta gaza wajen kula da wuraren da jama’a ke taruwa kamarsu tashar mota, kasuwanni dss.
“Babu cibiyoyin gwaji a jahohi da dama, jahohi basu samun tallafi kowani iri daga gwamnatin tarayya duk da makudan kudaden da gwamnati ta kashe daga asusunta da wanda jama’a suka tara mata.
“Don haka mun gaza gane hikimar dake cikin matakin da gwamnati ta dauka na sassauta dokar ta bacin yayin da ake tsaka da wannan annobar duba da halin da wasu kasashe suka shiga bayan sassauta dokar.” Inji ta.
Daga karshe kungiyar ta jinjina ma gwamnonin Najeriya bisa namijin kokarin da suke yi wajen yaki da yaduwar cutar, inda ta ce sun yi kyawun kai tare da nuna kishin jama’ansu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng