Yanzu-yanzu: Mutum 238 sun sake kamuwa da Korona, jimillar ta haura 2,000

Yanzu-yanzu: Mutum 238 sun sake kamuwa da Korona, jimillar ta haura 2,000

Kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta bayyana, an samu karin mutum 238 wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a Najeriya a ranar Juma'a.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, jihar Kano ta samu karin mutum 92, babban birnin tarayya akwai karin mutum 36, jihar Legas ta samu karin mutum 30.

A jihar Gombe da ke yankin Arewa maso gabas an samu karin mutum 16 da ke dauke da cutar, sai kuma mutum 10 a jihar Bauchi.

Kamar yadda NCDC ta wallafa a shafinta na twitter, an samu karin mutum 8 a jihar Delta, jihar Oyo akwai mutum 6, jihohin Zamfara da Sokoto akwai karin biyar-biyar.

A jihohin Ondo da Nasarawa an samu karin mutum hurhudu, jihohin Kwara, Edo, Ekiti, Borno da Yobe an samu karin mutum uku-uku.

A jihar Adamawa an samu karin mutum biyu sai kuma jihohin Niger, Imo, Ebonyi, Ribas da Enugu sun samu karin mutum daddaya.

Kamar yadda jimilla ta bayyana, akwai mutum 2170 wadanda aka tabbatar da suna dauke da cutar korona a Najeriya.

An sallama majinyata 351 daga asibiti bayan sun warke yayin da mutum 68 suka riga mu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel