COVID-19: An tabbatar da kamuwar ministoci 3 da cutar Korona

COVID-19: An tabbatar da kamuwar ministoci 3 da cutar Korona

- An tabbatar da cewa Firam ministan kasar Guinea-Bissau tare da wasu ministoci uku sun harbu da kwayar cutar Korona

- Kamar yadda ministan lafiya na kasar, Antonio Deuna ya bayyana, an killace ministocin a wani otal da ke babban birnin kasar

-Bincike ya bayyana cewa, ministan harkokin cikin gida, Botche Cande tare da wasu sakatarorin gwamnatin kasar duk sun kamu

Firam ministan kasar Guinea-Bissau, Nunu Nabiam da wasu ministoci uku an tabbatar da sun kamu da cutar Covid-19 a ranar Laraba.

Ministan lafiya, Antonio Deuna ne ya tabbatar da hakan. Ya ce an killacesu ne a wani otal da ke babban birnin kasar, jaridar New Telegraph ta wallafa.

An gano cewa, wasu 'yan majalisar shugaban kasar da suka hada da ministan harkokin cikin gida, Botche Cande, sakatarorin gwamnatin biyu, Mario Fambe da Monica Buaro duk sun kamu.

A halin yanzu, kasar Guinea-Bissau ta tabbatar da kamuwar mutum 73 da cutar a kasar. Mutum daya ya rasu kuma 18 sun warke.

Shugaban kasa Umaro Sissico Embalo ya kara tsawaita dokar hana zirga-zirga a kasar don hana yaduwar Covid-19 har zuwa 11 ga watan Mayu.

Shugaban kasa Embalo ne ya nada Nabiam a matsayin Firam ministan kasar a karshen watan Fabrairun 2019.

COVID-19: An tabbatar da kamuwar ministoci 3 da cutar Korona
COVID-19: An tabbatar da kamuwar ministoci 3 da cutar Korona
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rikicin addini ya barke a tsakanin 'yan Najeriya da ke kasar Kamaru

A wani labari na daban, rikicin addini ya barke tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kiristanci a sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya da ke Kamaru.

Lamarin ya faru ne a sansanin Minawao a ranar Laraba.

Wannan lamarin ne ya kai ga rushe gidaje da kona wasu sassa biyu na masu adawa da juna, ballantana na mazauna shiyya ta biyu da ta uku na sansanin.

Hakazalika, sun ji wa juna miyagun rauni da makamai. Amma kuma jami'an tsaro sun shiga tsakaninsu don kawo lafawar rikicin.

Wakilin BBC a Kamaru ya ce akwai alamun da ke nuna cewa dukkan bangarorin 'yan asalin jihar Borno ne kuma sun fito ne daga kananan hukumomin Goza da Bama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel