Mayakan Boko Haram sun yi ma jami’in rundunar Sojin Chadi kisan gilla

Mayakan Boko Haram sun yi ma jami’in rundunar Sojin Chadi kisan gilla

Kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta musanta ikirarin da shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi na cewa ya fatattake su daga yankin tafkin Chadi.

Jaridar Punch ta ruwaito kungiyar ta bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ta saka inda ta nuna yadda ta yi ma jami’in Sojan kasar Chadi kisan gilla ta hanyar dirka masa harsashi a kai.

KU KARANTA: An kama matar da ta halaka uwar mijinta bayan ta caka ma ta wuka a jahar Neja

Jami’an gwamnatin kasar Chadi sun tabbatar da sahihancin bidiyon. Ko a cikin bidiyon an hangi mutumin da yan ta’addan suka kashe yana sanye da kakin Sojojin Chadi.

Shi ma dan ta’addan da ya yi harbin yace sun kama Sojan ne a keuyn Litri a wani samame da suka kai ma Sojojin Chadi a ranar 18 ga watan Afrilu, inda suka kashe Sojoji guda 2.

Mayakan Boko Haram sun yi ma jami’in rundunar Sojin Chadi kisan gilla

Mayakan Boko Haram sun yi ma jami’in rundunar Sojin Chadi kisan gilla
Source: Facebook

Wasu manyan hafsoshin Sojojin kasar Chadi sun tabbatar ma kamfanin dillancin labaru na AFP cewa mutumin da aka kashe a bidiyon na daga cikin Sojojin da suka bace bayan harin.

A shekarar 2016 ne ISWAP ta balle daga kungiyar Boko Haram, inda ta karkatar da hankalin ta wajen kai hare hare ga sansanin Sojoji tun daga shekarar 2018.

A ranar 23 ga watan Maris ne yan ta’addan ISWAP suka kai wani samame a sansanin Sojojin Chadi dake Bohoma inda suka kashe Sojoji 98.

Hakan ta sa shugaban kasar Chadi ya jagoranci wani babban samame daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu, harin da yace sun kashe fiye da yan ta’adda 1000 a cikinsa.

A hannu guda kuma, Allah Ya yi ma mai martaba Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar El-Kanemi rasuwa a ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, ranar azumin Ramadana na 4.

Gwamnatin jahar Borno ce ta tabbatar da mutuwar basaraken mai daraja na daya a jerin masarautun jahar Borno, inda tace ya rasu ne a wani asibiti dake Maiduguri.

Marigayi Kyari shi ne Shehun tsohuwa masarautar Dikwa na 7, wanda ya hada da kananan hukumomin Bama, Dikwa, Ngala da Kala-Balge.

A shekarar 2010 ne gwamnatin jahar Borno ta raba masarautar gida biyu zuwa Bama da Dikwa, kuma ta baiwa kowannensu Sarki mai daraja na daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel