Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa

- 'Yan majalisar wakilan Najeriya sun yi wa sakataren gwamnatin tarayya, Mustapha Boss, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa

- Majalisar na bukatar bayani dalla-dalla ne a kan mace-macen da ya addabi jihar Kano tun bayan barkewar annobar Covid-19 a jihar

- Sun samu kiran gaggawar ne a yau Talata bayan 'yan majalisar sun koma aiki

Majalisar wakilan Najeriya ta yi wa sakataren gwamnatin tarayya, Mustapha Boss, ministan lafiya da kuma shugaban NCDC kiran gaggawa.

Majalisar wakilan ta yi hakan ne don su yi mata bayani a kan mace-macen da ke aukuwa a jihar Kano.

Sun samu wannan kiran ne a yau din nan bayan komawarsu zaman majalisar da suka yi a yau Talata, gidan talabijin TVC ya ruwaito.

Kamar yadda hotuna suka nuna, an ga 'yan majalisar wakilan na kiyaye dokokin nisantar juna a zauren majalisar.

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna

Mambobin majalisar dokokin tarayya sun dawo zaman majalisa bayan kimanin makonni biyar da tafiya hutu a kan annobar coronavirus.

Yan majalisa na dattawa da na wakilai sun koma zauren majalisar a Abuja, a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, bayan sun tafi hutu duk a cikin matakan hana yaduwar cutar COVID-19 a kasar.

A majalisar wakilan, shugaban majalisa wakilan , Femi Gbajabiamila ya jagoranci mambobinta zuwa zauren, inda aka fara tattaunawa da misalin karfe 10:30 na safe, jim kadan bayan sun samu waje sun zazzauna.

A yayin da ake tsaka da samun hauhawar masu COVID-19 a kasar, an bukaci 'yan majalisar su bayar da tazara a tsakaninsu ta hanyar tsallake kujeru bibbiyu wajen zamansu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar wakilai ta tsayar da ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2020, a matsayin ranar da zata dawo daga hutun da ta tafi.

Jaridar 'OderPaperNG' ta rawaito cewa ta ga sakonnin sanarwa da aka aike wa mambobin majalisar da yammacin ranar Lahadi.

A cikin sakon sanarwar mai dauke da sa hannun Patrick A. Giwa, magatakardar majalisa, an shawarci sauran hadiman mambobin majalisa su cigaba da zama a gida har zuwa sanarwa ta gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel