Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 89 a Zamfara, sun halaka wasu a Katsina

Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 89 a Zamfara, sun halaka wasu a Katsina

Rundunar sojin Operation Hadarin Daji ta halaka 'yan bindiga 89 tare da ceto wasu mutum biyar da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo janar John Enenche, ya ce nasarar da rundunar ta samu ta sameta ne tare da hadin guiwar bataliya ta 35 da kuma kungiyar taimakon gaggawa ta Rundunar sojin Najeriyan.

Ya ce a arangamar da rundunar ta yi da 'yan bindigar a ranar 24 ga watan Afirilun 2020, sun samu kwace makamai a wurin Gidan Jaji da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Ya kara da cewa, wadanda aka yi garkuwa da su din sun hada da mata uku da maza biyu.

Kayayyakin da suka samu daga hannun 'yan ta'addan sun hada da bindiga kirar AK 47 guda 29, PKT daya, carbi tara na harsashi, nadi 167 na harsashi na musamman da kuma wata bindiga fiston daya.

Ya ce a yayin da ba a samu rai ko daya da aka rasa ba, sun samu shanu 322 na sata, babur 77 da kuma wayoyi 9.

Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 89 a Zamfara, sun halaka wasu a Katsina
Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 89 a Zamfara, sun halaka wasu a Katsina
Asali: UGC

KU KARANTA: Covid-19: Minstan FCT ya saka sabuwar doka a kasuwanni

Ya ce za a mika shanun satan da kuma mutanen da suka ceta bayan sun bi ka'idojin da suka dace.

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, a wani ci gaba na daban, rundunar hadin guiwa da ke dajin iyakar jihar Katsina da Zamfara sun yi nasarar halaka 'yan bindiga masu tarin yawa.

Sun yi nasarar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa dasu.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ne ya bayyana hakan yayin karbar wadanda aka yi garkuwa dasu din daga wurin wakilin kwamandan birged na 17 da ke Katsina, Birgediya Janar B. Idris a jiya.

Ya ce wannan ya biyo bayan kokarin rundunar sojin sama da ta kasa a Katsina da Zamfara.

Kamar yadda yace, ruwan wutar ya kawo karshen rayuwar 'yan bindiga masu tarin yawa yayin da wasu daga cikin suka tsere.

Rashin maboya ne yasa suka fada hannun dakarun sojin da ke zagaye dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel