An samu matsala: Maganin da aka samar don warkar da cutar Corona ya ki aiki a jikin dan Adam

An samu matsala: Maganin da aka samar don warkar da cutar Corona ya ki aiki a jikin dan Adam

Tun bayan bullar kwayar cutar Coronavirus a garin Wuhan dake cikin lardin Hubei na kasar China a watan Disambar shekarar 2019 ne masana suke ta kokarin samar da maganinsa.

Bukatar maganin ya fi kamari a yanzu duba da dimbin mutanen da cutar ta yi ma illa, zuwa ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, annobar Coronavirus ta watsu a kusan kasashen duniya 200.

KU KARANTA: Dubi wasu kasashe guda 15 a Duniya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba

Maganan da ake a yanzu shi ne, Coronavirus ta harbi fiye da mutane miliyan 2.5, kuma ta kashe mutane 85,504, yayin da wasu mutane 730,843 suka samu waraka daga gare ta.

An samu matsala: Maganin da aka samar don warkar da cutar Corona ya ki aiki a jikin dan Adam

Maganin, daga hotunan Reuters
Source: Facebook

Wannan tasa masana ilimin kimiyya da sarrafa magunguna suka shiga bincike tare da gudanar da gwaje gwaje don samun takamaime kuma sahihin maganin cutar.

Da yake cutar sabuwa ce, don haka wasu kasashe suke daukan ta su sanya ma mutanen da suka amince a jikkunansu domin su karance ta tare da sanin hanyoyin maganinta.

Amma sakamakon maganin farko da aka fara samarwa da ake tunanin zai warkar da cutar daga jikin masu dauke da ita ya gaza biyan bukata, inji rahoton BBC.

Wannan magani mai suna Remdesivir an samar da shi ne a kasar Amurka, kuma an gwada shi a kan wani mai dauke da cutar a kasar China, sai dai ya gaza wajen maganin ta.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da gazawar maganin, saboda a cewarta, maganain bai hana kwayar cutar COVID-19 zagaye a cikin jinin mai dauke da cutar ba.

Sai dai wata kamfanin kasar Amurka dake goyon bayan maganin, Gilead Sciences ta musanta batun WHO, inda ta zargi WHO da canza ma’anar maganin.

A wani labari kuma, akwai wasu kasashe 15 da basu samu bullar Coronavirus a cikinsu ba, daga cikin wadannan kasashe akwai 2 a nahiyar Afirka; Lesotho da Comoros.

Sauran su ne: Kiribati, Marshall Islands, Federated States of Micronesia, Nauru, Palau Samoa, Solomon Islands, Tajikistan, Tonga, Turkmenistan, Tuvalu, Vanuatu da Koriya ta Arewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel