Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura

Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura

- A ta'aziyyar da Malam Mamman Daura ya rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya a kan Marigayi Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa

- Malam Mamman Daura ya bayyana cewa akwai lokacin da wasu kungiyoyin mata da matasa suka bukaci ya zama abokin tafiyar Obasanjo a 1999

- Kamar yadda Mamman Daura ya bayyana, Malam Abba Kyari mutum ne haziki kuma mai jajircewa

Mamman Daura, ya ce an bukaci Abba Kyari ya zama mataimakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a shekarar 1999.

Kyari, wanda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus da yayi a ranar 18 ga watan Afirilun 2020, shine shugaban ma'aikatan fadar shugaba Buhari.

A ta'aziyyarsa da Daura ya yi, ya kwatanta Kyari da mutum mai matukar hazaka wanda ya kusan zama mataimakin shugaban kasa a 1999.

"Wannan lokacin ya yi daidai da lokacin da kasar nan ta koma mulkin damokaradiyya kuma Abba Kyari na daga cikin na gaba a karfafa Janar Obasanjo.

"Bayan bayyanar Obasanjo a matsayin dan takara a jam'iyyar PDP, wata kungiyar mata da matasa sun dinga rokon Obasanjo a kan ya dauka Abba Kyari a matsayin abokin takara.

"Bayan tsananin muhawara da ta biyo baya, Obasanjo ya dauka Alhaji Atiku Abubakar a matsayin abokin tafiyarsa," Daura yace.

Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura

Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura
Source: Twitter

KU KARANTA: Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

Kamar yadda Daura ya sanar, A zaben 2003, Malam Abba ya koma jam'iyyar adawa.

Janar Muhammadu Buhari ya bayyana bukatarsa ta fitowa takarar shugabancin kasa kuma Malam Abba ya shiga cikin masu kamfen da dukkan iyawarsu.

Daura ya ce, Abba ya jajirce tun daga farko har sai da ya ga Buhari ya haye karagar mulkin kasar nan.

"Babban abin mamaki ga Abba shine yadda Buhari ya zabesa a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa.

"Sakamakon gogewarsa a jami'ar Cambridge, banki da sauran wuraren da yayi aiki, Malam Abba ya shirya don daidaituwa a mukaminsa.

"Ya fara ne da tuntubar wadanda suka taba rike kujerar don samun bayanai a kan kalubalen da zai iya fuskanta," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel