Sakon fara azumi: Buhari ya gargadi al'ummar Musulmi

Sakon fara azumi: Buhari ya gargadi al'ummar Musulmi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon fatan alheri ga dukkan Musulman Najeriya da na duniya baki daya a yayin da za su fara azumin kwana 30, biyo bayan ganin watan Ramadan.

"Ina taya duk Musulmi muranar zuwan azumin watan Ramadan, watan rahama, jin kai da taimakon mabukata," a cewar Buhari, kamar yadda kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fada.

Shugaba Buhari ya bayyana azumin shekarar 2020 a matsayin mai cike da kalubale, saboda ya zo a cikin annobar da ta yadu zuwa kasashen duniya 200, lamarin da ya sa kasashe daukan tsauraran matakai.

A cewar shugaba Buhari, kusan duk kasashen duniya sun shawarci jama'arsu a kan su kauracewa taron jama'a da yawa, su gudanar da salloli da addu'o'i a gidajensu.

Sakon fara azumi: Buhari ya gargadi al'ummar Musulmi
Shugaba Buhari
Asali: Twitter

"Ku sani cewa, a wannan lokaci, za ku yi azumi ne cikin kadaici, ba tare da walwala da nishadin da aka saba yi ba a lokutan baya," a cewarsa.

Shugaba Buhari ya ja hankalin Musulmi su guji shirya duk wani taron jama'a da sauran al'adu da aka saba yi a cikin watan azumi.

DUBA WANNAN: Covid-19: Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

A cewar shugaba Buhari, shugabannin addinin Musulunci a fadin duniya sun shawarci Musulmai su guji salloli a cikin jam'i ko tara jama'a domin cin liyafa yayin buda baki.

Shugaba Buhari ya bukaci Musulmai su nuna juriya tare da ba su shawarar kar su fake da annobar cutar covid-19 domin kin yin azumin watan Ramadana.

Ya yi wa Musulmin Najeriya da na duniya fatan alheri tare da samun rahamar da ke cikin watan Ramadana, wata mai tsarki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel