Jami'ai sun damko mutum 2 da suka gudu daga cibiyar killacewa a gidan giya

Jami'ai sun damko mutum 2 da suka gudu daga cibiyar killacewa a gidan giya

- Jami'an 'yan sandan kasar Kenya sun tabbatar da damke wasu mutum biyu a gidan giya bayan sun gudu daga cibiyar killacewa ta jihar

- Kamar yadda BBC ta wallafa, mutum biyun na daga cikin a kalla mutane 50 da suka tsere daga cibiyar killacewar da ke Nairobi

- A yayin da aka umarci dukkan mashaya da ke kasar da su rufe don gujewa yaduwar cutar, an zargi cewa mutum biyun sun hada baki ne da mai mashayar

Jami’an ‘yan sandan kasar Kenya sun kama wasu mutum 2 da suka tsere daga cibiyar killacewa a gidan giya.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, mutum 2 na daga cikin mutane fiye da 12 da aka gano sun haure katangar cibiyar killacewa ta Nairobi bayan suna dauke da cutar Covid-19.

An gano cewa, ‘yan sandan sun damke mutum biyun ne a wata mashaya da ke yankin Roysambu inda suke ta faman dirkar giyarsu.

A yayin da aka umarci dukkan mashayar da ke kasar da su rufe don gujewa yaduwar cutar, an zargi cewa mutum biyun sun hada baki ne da mai mashayar.

An gano cewa mutum biyun da aka bukaci su biya dala 20 zuwa dala 100 sun kasa biyan kudin giyar da suka sha.

DUBA WANNAN: COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki

An gano cewa, a kalla mutum 400 ne aka killace sakamakon karya dokar ta baci da hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta kafa.

A kalla mutum 50 ne aka gano cewa sun haura katangar cibiyar killacewar amma da yawansu an damko su.

“Da yawa daga cikin wadanda suka tsere an kama su a kusa da cibiyar killacewar kafin su shiga gari. Mun san sauran za su shigo hannu," Muthuri Mwongera, wani dan sandan kasar ya tabbatar.

A wani labari na daban, a ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ce ya warke daga muguwar cutar coronavirus bayan gwaji har kashi biyu sun nuna babu cutar a tare da shi.

El-Rufai a matsayin wanda ya yi nasarar samun lafiya, ya kwatanta cutar da babban kalubale ga jama'a. Ya ce ba zai yi wa babban makiyinsa fatan samun cutar ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel