Covid-19: A yau za a sake gwada ma'aikatan lafiyan China a Najeriya - Ehanire

Covid-19: A yau za a sake gwada ma'aikatan lafiyan China a Najeriya - Ehanire

- Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya ce a yau za a sake gwada ma'aikatan lafiya da suka zo Najeriya daga kasar China a kan kwayar cutar coronavirus

- Ma'aikatan lafiyan, wadanda suka iso Najeriya dauke da kayan dala miliyan 1.5 an killacesu na kwanaki 14 tun bayan isowarsu kasar nan

- Ma'aikatan lafiyan sun hada da likitoci, ma'aikatan jinya da kuma masu gwaji wadanda suka zo don bayyanawa ma'aikatan lafiyar kasar nan yadda suka yaki cutar

Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya ce a yau za a sake gwada ma'aikatan lafiya da suka zo Najeriya daga kasar China a kan kwayar cutar coronavirus.

Ma'aikatan lafiyan, wadanda suka iso Najeriya dauke da kayan dala miliyan 1.5 an killacesu na kwanaki 14 tun bayan isowarsu kasar nan.

Ma'aikatan lafiyan sun hada da likitoci, ma'aikatan jinya da kuma masu gwaji wadanda suka zo don bayyanawa ma'aikatan lafiyar kasar nan yadda suka yaki cutar.

A yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar coronavirus, Ehanire ya ce: "Na bada umarnin a yi gwaji ga ma'aikatan lafiya da suka iso Najeriya kuma za mu san ingancin lafiyarsu kafin su fara aiki."

Ya ja kunnen masu shagunan magani ko talla a kan bai wa masu cutar coronavirus magani, ko kuma a kwace lasisinsu.

Ehanire ya ce daga yanzu duk inda cutar ta kama mutum, a nan za a bashi magani a maimakon mayar da shi jiharsa.

Covid-19: A yau za a sake gwada ma'aikatan lafiyan China a Najeriya - Ehanire
Covid-19: A yau za a sake gwada ma'aikatan lafiyan China a Najeriya - Ehanire
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano

Ministan ya ce, "Sai dai idan akwai wani dalili na daban. Hakan zai iya kawo yaduwar cutar ga marasa ita a yayin kai mai ita jiharsa."

A wani labari na daban, an ji cewa a jiya an ga mutane masu tarin yawa a kasuwannin birnin tarayya suna karya dokar gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta lura cewa an karya dokokin nisantar juna a kasuwannin Garki, Wuse, Nyanya da Karu.

'Yan kasuwa da masu siyayya sun take dokar nisantar juna inda suke ta hada-hadarsu.

Ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello ya rage kwanakin zuwa kasuwa inda ya mayar da su kwanaki biyu kacal a cikin mako.

Hatta direbobi a kan manyan tituna sun take dokar da gwamnatin ta saka na daukar jama'a kadan a cikin motocin haya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel