Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi

Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA, dake karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, ta ki amincewa da matakin kona gawar Musulmin da Coronavirus ta kashe.

Daraktan gudanarwa na NSCIA, Yusuf Nwoha, ne ya bayyana haka a ranar Talata, yayin bayani game da abin da ya kamata a yi da gawar Musulmin da annobar ta kashe.

KU KARANTA: Miyagun yan bindiga sun kashe Yansanda 2 a cikin kamfanin Atiku Abubakar

Wasu rahotanni sun bayyana yadda ake kona gawar duk mutumin da Corona ta kashe ne domin gudun yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi
Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi
Asali: Facebook

A jawabinsa, Nwoha yace Musulunci bai yarda da kona gawar Musulmi da gangan a kowanne hali ba, don haka bai kamata a kona gawar Musulmin da ya rasu a dalilin cutar Coronavirus ba.

Ya kara da cewa wanke gawa da ake yi, Musulunci ya tanade shi ne domin tsaftace gawar daga dukkanin wasu cututtuka da wasu zasu iya dauka daga kanta.

“Dokar ita ce kada a bar wani abu da zai cuci al’umma, idan kuma mamacin yana dauke da cutar da za’a iya dauka, hakkin gwamnati ne ta shirya shi ta hanyar watsa masa ruwan wankan har ya taba ko ina a jikinsa, ko kuma a kwarara ma gawar ruwan ba tare da an cuccuda ba.

“Ba lallai bane sai an shirya shi a cikin likafani da wani tsari, idan har likafanin ta rufe ko ina da ko ina a jikinsa, ya wadatar, amma idan zai yiwu, ayi amfani da falle uku ko biyar na likafanin ga namiji, falle biyar ga mace.” Inji shi.

Ya cigaba da cewa: “Babu laifi idan an sanya mutum cikin jakar gawa don gudun yaduwar cutar, amma idan da hali kalar jakar ta zama fara, ko kuma a saka mutum a akwatin gawa duk a cikin matakan kare yaduwar. Hakkin gwamnati ne ta sanya idanu a kan duk abin nan da aka yi ma gawar.”

Daga karshe ya ce amma idan har an tabbatar da cewa babu wata cutar da za a iya dauka a jikin gawar, dole ne a yi masa wanka da sitira kamar yadda ake yi ma kowa.

Sai dai jama’a kadan sun wadatar a wajen jana’izarsa da kuma binne shi, saboda dokar hana cudanya da mutane da yawa da kuma ta hana shige da fice.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel