Dubi wasu jahohi guda 12 a Najeriya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba

Dubi wasu jahohi guda 12 a Najeriya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba

Duk da yadda annobar Coronavirus ke cigaba da yaduwa a Najeriya kamar wutar kara, akwai wasu jahohi guda goma sha biyu da har yanzu ba’a samu bullar cutar a cikinsu ba.

Jaridar Punch ta ruwaito zuwa yanzu cutar Coronavirus ta shiga jahohi 25 da kuma babban birnin tarayya Abuja, inda ta kama mutane 782, ta kashe 25.

KU KARANTA: Sojoji sun yi ma yan bindiga ruwan bamabamai a wani kauyen Neja

Wadannan jahohi da cutar bata ratsa su ba sun hada da: Adamawa, Bayelsa, Cross River, Ebonyi, Imo, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Plateau, Taraba, Yobe da kuma jahar Zamfara

Sai dai duk da haka gwamnatocin jahohin basu yi kasa a gwiwa ba, suna cigaba da daukan matakan kandagarki domin kuwa annobar babu ruwanta da jaha ko jam’iyya.

Dubi wasu jahohi guda 12 a Najeriya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba
Dubi wasu jahohi guda 12 a Najeriya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba
Asali: UGC

A yanzu gwamnonin jahar Plateau, Nassarawa, Yobe da Imo sun garkame iyakokin jahohinsu babu shiga babu fita, wannan wani mataki ne na kare baki daga shigar musu da cutar.

A hannu guda kuma, hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC ta sanar da samun karuwar sabbin mutane 117 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

“Zuwa karfe 11:25 na daren Talata, 21 ga watan Afrilu, akwai mutane 782 da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 da aka samu rahotonsu a Najeriya, 25 sun mutu, yayin da an sallami 197.” Inji NCDC.

Jahohin da aka samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun hada da jahar Legas – 59, Kano 29, Borno 6, Katsina 4, Ogun 3, Rivers 1, da jahar Bauchi 1.

Ga jerin jahohin da cutar ta shiga da adadin mutanen da ta kama kamar haka; Legas-430, Abuja – 118, Kano- 73, Osun- 20, Edo- 15, Oyo- 16, Ogun- 20, Katsina- 16, Bauchi- 8, Kaduna- 9.

Sai kuma Akwa Ibom- 9 da Kwara-9, Borno-9, Delta- 4, Ondo- 3, Enugu- 2, Ekiti- 4, Rivers-3, Ondo- 3, Niger – 2, Benue- 1, Jigawa – 2, Gombe – 5, Sokoto – 1, Abia – 2, sai jahar Anambra- 1.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel